Tudun Biri: Hanyoyi 5 Sojoji Za Su Bi a Kiyaye Kashe Bayin Allah, Farfesa Pantami

Tudun Biri: Hanyoyi 5 Sojoji Za Su Bi a Kiyaye Kashe Bayin Allah, Farfesa Pantami

  • Isa Ali Ibrahim Pantami ya sake yin magana ganin yadda sojoji su ka kashe masu maulidi wajen neman ‘yan ta’adda
  • Farfesan ya ba sojoji shawarar akwai fasahohin zamani da ake amfani da su domin a gujewa kashe Bayin Allah
  • Pantami ya fadi irin kayan aikin da ya dace a nema, kuma ya bukaci a horar da masu amfani da jirage na ‘drone’

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Isa Ali Ibrahim Pantami wanda ya yi shekaru kusan hudu a kujerar minista, ya sake magana a kan abin da ya faru a Tudun Biri.

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamanin ya ba sojoji shawara a Twitter, ya yi bayanin yadda za a kiyaye jefawa mutane bam.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi maganar kisan masu Maulidi, ya fadi nasarar farko da aka samu

Prof. Isa Ali Ibrahim, CON
Isa Ali Ibrahim, CON ya yi kira ga sojoji Hoto: @ProfIsaPantami
Asali: Twitter

Sojoji sun ce kuskure aka yi har aka kashe mutane kusan 100 a kauyen Tudun Biri a lokacin da dakaru ke kokarin ganin bayan ‘yan bindiga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kaduna: Isa Ibrahim Pantami ya yabi Lagbaja

Farfesa Isa Ibrahim Pantami ya ce ya saurari jawabin Laftanan Janar Taoreed Lagbaja a sa’ilin da ya kai ziyara zuwa kauyen da abin ya faru.

Malamin musuluncin ya yabawa hafsun sojojin ganin yadda ya yi maza ya ziyarci Tudun Biri.

A jawabin da ya yi a Twitter, baya ga ta’aziyyar mutanen da aka rasa wajen maulidi, Ministan ya ce ya taba jami’an tsaro shawara a 2020.

Shawarar Farfesa Pantami ga sojojin kasa

"Na farko za a iya magance wannan kuskure cikin sauki a zamanin nan na fasahar 4IR ko Industry 4.0 da aka shigo da su
Yayin da ake da fasahar da su ka fito irinsu AI ko ilmin na’urori, za a iya samun tabbaci wajen amfani da jirgi mara matuki da sauran kayan aikin sojoji

Kara karanta wannan

Yanzu: An nemi ministan tsaron Tinubu ya yi murabus kan kisan masu Maulidi a Kaduna

Na biyu, wajen amfani da tsarin AI, sojoji za su iya yin abin da ake kira ‘gane abokin fada’ wanda zai bada kusan tabbacin 100%.
Za a iya amfani da AI wajen gane bayanai, a tantance kuma a ware wadanda za a kai wa hari.
Sannan ana bada shawara mai karfi cewa idan babu tabbaci 100% ne, a fasa kai hari.

- Isa Ali Ibrahim (Pantami), CON, FCIIS, FBCS, FNCS

Pantami ya ce akwai kayan aiki na musamman

Pantami ya ce da fasahar zamanin yau, ana iya ganin wurin da mutane su ke, abubuwan hawansu domin a bambanta su da ‘yan bindiga.

Har wa yau tsohon ministan ya kawo sunayen na’urorin da za a iya amfani da su, na biyar ya ce sai an horar da masu aiki da jirage mara matuku.

Sanusi ya yi wa mutanen Tudun Biri ta'aziyya

Muhammadu Sanusi II ya yi wa al’umma ta’aziyyar rayukan Musulmai da aka rasa wajen maulidi a Kaduna a matsayinsa na Khalifan Tijjaniya.

Sanusi II ya kira wadanda su ka rasu masu shahada, ya ce bai dace irin wannan ya sake faruwa ba, an rahoto ya na cewa wajibi ne ayi bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel