Assha: Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 4 a Plateau, Sun Kona Gidan Basarake

Assha: Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 4 a Plateau, Sun Kona Gidan Basarake

  • Rundunar soji ta yi nasarar ceto iyalan gidan sarkin kauyen Dungwel da ke karamar hukumar Mangu, jihar Plateau daga harin 'yan bindiga
  • A yammacin ranar Lahadi ne 'yan bindigaN suka shiga kauyen Dungwel, inda suka kashe mutum hudu da kone gidan sarkin garin
  • Rundunar soji ta ce ta isa garin da gaggawa, inda ta ceto mata da kananan yara daga gidan basaraken da 'yan bindiga suka cinnawa wuta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Plateau - Wasu 'yan bindiga sun kashe mutum hudu a kauyen Dungwel, karamar hukumar Mangu da ke jihar Plateau , a yammacin ranar Lahadi.

Daya daga cikin wadanda abin ya shafa, Shedrack Gambo, ya shaidawa jaridar The Punch cewa mutum 4 sun mutu a harin, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun tashi wani kauyen Abuja bayan kashe mutum 1 da neman fansar N5m

Yan bindiga sun kai hari Plateau, sun kashe mutum 4
Sojoji sun bayyana cewa 'yan bindigar sun kone gidan basaraken garin Plateau da iyalinsa a ciki, amma sun kubutar da su. Hoto: Nigeria Army
Asali: Twitter

Gambo ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Duk sun mutu nan take kuma wasu sun jikkata. Al'ummar garin na cikin jimami da tashin hankali, ku taya mu da addu'a."

Me ya kai 'yan bindiga garin Dungwel?

A ranar Litinin a garin Jos, mai magana da yawun tawagar jami'an soji, Keftin Oya James, ya tabbatar da kai harin 'yan bindigar da kuma kone gidan basaraken.

"Na kira shugaban FOB kuma ya tabbatar da mutum hudu suka mutu, inda suka gano 'yan bindigar sun je garin don farmakar sarkin garin.
"A cewar rahoton dakarun, 'yan bindigar sun shiga garin suna tambayar gidan basaraken, daga nan ne mutane suka fara rantawa a na kare."

A cewar shugaban tawagar sojin.

Keftin James ya kara da cewa 'yan bindigar sun kone gidan basaraken da iyalinsa a ciki, amma dakarun soji sun kubutar da su.

Kara karanta wannan

Ba a gama da jimamin kashe masu maulidi ba, 'yan bindiga sun yi kazamin barna a Bauchi

Yan bindiga sun tashi wani kauyen Abuja, sun kashe mutum 1

A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta ruwaito maku yadda al'ummar garin Yewuti da ke babban birnin tarayya Abuja suka yi hijira zuwa wasu garuruwa.

A cewar mazauna garin, hijirar ta zama dole saboda yawan hare-haren da 'yan bindiga ke kai masu.

A baya-bayan nan ne 'yan bindiga suka kai farmaki garin, inda suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu hudu har sai da aka biya kudin fansa Naira miliyan biyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel