‘Yan Majalisan Arewa Sun Yi Koyi da Sanatoci, Sun bada N350m ga Wadanda Sojoji Su Ka Kashe

‘Yan Majalisan Arewa Sun Yi Koyi da Sanatoci, Sun bada N350m ga Wadanda Sojoji Su Ka Kashe

  • ‘Yan Majalisar Arewa a karkashin jagorancin Alhassan Ado Doguwa za su kashe N350m a garin Tudun Biri
  • Shugaban majalisar wakilai, Dr. Tajuddeen Abbas da ragowar ‘yan majalisar Kaduna sun ba mutanen N45m
  • Hon. Ado Doguwa ya ce ‘yan majalisar da su ka fito daga Kudancin kasar nan za su tara masu gudumuwar N30m

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - ‘Yan majalisan da su ka fito daga jihohin Arewacin Najeriya sun sha alwashin taimakawa ‘yan garin Tudun Biri a jihar Kaduna.

A ranar Litinin aka samu labari daga Tribune cewa ‘yan majalisan kasar za su ba mutanen Tudun Biri gudumuwar N350m domin tallafa masu.

'Yan majalisa a Tudun Birni
'Yan majalisa sun je Tudun Birni Hoto: @aadoguwa
Asali: Twitter

Shugaban ‘yan majalisar yankin, Alhassan Ado Doguwa ya yi wannan alkawari a jiya da ya jagoranci ‘yan majalisa zuwa garin da abin ya faru.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 3 da suka faru gabanin yan Majalisa 27 su sauya sheka daga PDP zuwa APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Honarabul Ado Doguwa da ‘yan tawagarsa sun ziyarci kauyen da ke karamar hukumar Igabi mako guda da kashe Bayin Allah kusan 100.

Karin N350m a kan N45m a Tudun Biri

‘Dan majalisar na Tudun Wada/Doguwa ya ce wannan kudin kari ne kan N45m da shugaban majalisa da ‘yan majalisar jihar Kaduna su ka bada.

An rahoto tsohon shugaban masu rinjayen majalisar wakilan yana cewa sauran ‘yan majalsan yankin Kudu za su kawo masu taimakon N30m.

Tudun Biri: 'Yan majalisa sun yabawa Tinubu

Doguwa ya jinjinawa matakan da gwamnatin Bola Tinubu ta dauka na tuntubar wadanda wannan masifa ta auka masu domin a kula da su.

Punch ta ce ‘yan majalisar na Arewa sun kuma ji dadin yadda za a sake gina garin, tare da kira a tabbata an biya dangi diyyar da aka yi alkawari.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun kai samame fadar babban sarki, sun kwato makamai

Gwamnati na cigaba da taimakawa al'umma

Gwamnatin tarayya za ta yi ayyukan more rayuwa a wannan kauye da su ka hada da makarantu, asibiti, ruwan shan da samar wutar lantarki.

Da aka je asibitin koyar da aiki na Barau Dikko domin ganin wadanda su ke jinya, Hon. Doguwa ya bada N1m domin a cigaba da kula da su.

El-Rufai ya wuce Daura daga Tudun Biri

Bayan ziyarar da ya kai zuwa Tudun Biri, Malam Nasir El-Rufai da mutanensa sun je garin Daura a Katsina domin gaida Muhammadu Buhari.

An rage jin duriyar tsohon gwamnan tun da aka cire shi daga sunan wadanda za a ba Ministoci da Bola Tinubu ya samu shugabancin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel