Zaben jihohi
Mutane masu kaɗa kuri'a sun garkame ma'aikatan zaɓe a gundjmar Oko II, ƙaramar hukumar Orumba North lokacin da suka so guduwa daga wurin zuwa karamar hukuma
A yau Asabar ne jama'ar jihar Anambra za su fito kwansu da kwarkwata domin zaben gwamnan da zai shugabancesu nan da shekaru hudu. Akwai 'yan takara 18 a zaben.
Daya daga cikin babbar matsalar da ke cigaba da haifar da matsala a Najeriya shi ne siyan kuri'a, wanda kuma ya cika a zaben gwamnan jihar Anambra da ake yi.
Anambra - Dan takaran jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Charles Soludo, ya bi manyan abokan hamayyarsa karamar hukumarsu kuma ya lallasa su.
Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan babban bankin Najeriyan ya isa rumfar zabensa da wuri amma ya kasa saka kuri'arsa saboda rashin aikin da na'urar BVAS.
An fara kada kuri'a a yawancin yankunan Awka, babban birnin jihar Anambra inda aka girke jami'an tsaro da yawa a yankin duk da karancin fitowar masu yin zabe.
Masu yin zabe da dama a jihar Anambra sun kauracewa rumfunan kada kuri'u a zaben gwamnan Anambra da ke gudana a yanzu haka a yau Asabar, 6 ga watan Nuwamba.
Kwamishinan labarai da wayar da kan jama'a na jihar Anambra, Mista Don Adinuba, ya ce rahoton da ke yawo cewa mutane na barin jihar gabannin zabe karya ne.
A cikin watannin da suka gabata, tsaro a jihar ya lalace, lamarin da ya dinga zama kalubale tare da tunanin yadda zaben zai kasance a yankin da kasar baki daya.
Zaben jihohi
Samu kari