Zaben Anambra: Buhari ya taya Soludo murnar lashe zaben gwamnan Anambra

Zaben Anambra: Buhari ya taya Soludo murnar lashe zaben gwamnan Anambra

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Charles Soludo murnar lashe zaben gwamna a jihar Anambra
  • Shugaban ya bukaci Soludo da ya hada kan jama'ar jihar domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali
  • Hakazalika, Buhari ya yabawa jami'an tsaro da na hukumar INEC kan aikin da suka yi ba tare da an samu matsala ba

Abuja - Shugaban kasan Najeriya, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya taya tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Farfesa Charles Soludo, murnar lashe zaben gwamnan Anambra na 2021.

A ranar Asabar ne aka kada kuri'ar zaben gwamnan jihar Anambra, wanda yayi tsawo sai yau Laraba aka sanar da sakamakon zaben.

Zaben Anambra: Buhari ya taya Soludo murnar lashe zaben gwamnan Anambra
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari | Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

Da yake taya Soludo murna, shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:

"Ina taya Farfesa Charles Chukwuma Soludo, dan takarar jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) - kuma mamba a kwamitin ba da shawara kan tattalin arziki na shugaban kasa (PEAC) - bisa nasarar da ya samu a zaben gwamnan jihar Anambra."

Read also

Dan takarar gwamnan PDP ya amince da shan kaye, ya taya Soludo murna

Hakazalika, shuga Buhari ya yabawa jami'an tsaro da na INEC bisa kokarin da suka yi wajen tabbatar da zabe mai inganci duk kalubalen tsaro a jihar.

A bangare guda, shugaba Buhari ya bukaci Soludo ya yi kokarin shawo kan kalubalen da ya addabi jihar da ma yankin kudu maso gabas.

A cewarsa:

"Ina kira ga Farfesa Soludo da ya hada kan sauran masu ruwa da tsaki don tunkarar manyan kalubalen da ke fuskantar jihar Anambra da kuma Kudu maso Gabas gaba daya.

Hakazalika, shugaba Buhari ya ce ya shirya aiki tare da Soludo don wanzar da zaman lafiya a jihar.

Shugaba Buhari ya kara da cewa:

"Ina fatan yin aiki tare da shi don samar da zaman lafiya, tsaro da ci gaban jihar Anambra da kasa baki daya."

Read also

Zaben Anambra: Soludo ya shiga sahun su Ganduje, gwamnonin Najeriya masu PhD

Soludo ne ya lashe zaben gwamnan da ya kammala yau Laraba tare da samun kuri'u sama da dubu dari.

Hakazalika, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan Anambra da aka kammala, Valentine Ozigbo, a ranar Laraba ya amince da shan kaye tare da taya dan takarar jam’iyyar APGA, Chukwuma Soludo murnar lashe zabe, Punch ta ruwaito.

Soludo mai shekaru 61 ya samu nasara da kuri’u 112,229 inda ya doke Ozigbo wanda ya samu kuri’u 53,807 da Andy Uba na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 43,285 da kuma Ifeanyi Ubah na jam'iyyar YPP da ya samu kuri'u 21,261 wanda ya zo na hudu.

Zaben Anambra: Dalilai 5 da suka sa PDP ta sha mummunan kaye a zaben gwamna

A wani labarin, dan takarar jam'iyyar adawa ta PDP Valentine Ozigbo ya lashe karamar hukuma daya kacal a kada kuri'a da aka yi.

Ozigbo ya samu kuri’u 3,445 inda ya doke Chukwuma Soludo, dan takarar jam’iyyar APGA, wanda ya samu kuri’u 3,051, yayin da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu kuri’u 1,178 a karamar hukumar Ogbaru.

Read also

Da duminsa: Soludo ya magantu bayan lashe zaben Anambra

Wannan shine nasara ta farko da PDP ta samu a tsakanin kananan hukumomin jihar da aka kada kuri'a a zaben na gwamna.

Source: Legit.ng

Online view pixel