Da duminsa: Wasu jami'an INEC sun kauracewa zaben Ihiala a Anambra

Da duminsa: Wasu jami'an INEC sun kauracewa zaben Ihiala a Anambra

  • Wasu daga cikin jami'an INEC na wucin-gadi sun kauracewa zaben karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra
  • Da yawa daga cikin jami'an wucin-gadin 'yan bautar kasa ne wadanda aka horar domin aikin zaben gwamnan
  • Matsalar tsaro ce ta hana yin zaben a ranar Asabar, hakazalika matsalar ce ta sa 'yan bautar kasan suka ki zuwa

Anambra - Wasu jami'an wucin-gadi na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da aka tura karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra sun kauracewa rumfunan zabensu saboda matsalar tsaro.

A ranar Asabar da ta gabata, ba a yi zabe ba a karamar hukumar Ihiala saboda matsalar tsaro, Daily Trust ta wallafa.

A yayin bayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba, Farfesa Comfort Obi, baturiyar zaben jihar, ta ce hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, ba ta tura kayayyakin zabe ba saboda rahoton halin da ake ciki da ta samu.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Mata ta haihu jim kadan bayan kada kuri'a, ta rada masa suna Soludo

Da duminsa: Wasu jami'an INEC sun kauracewa zaben Ihiala a Anambra
Da duminsa: Wasu jami'an INEC sun kauracewa zaben Ihiala a Anambra. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ce EO ya tabbatar da cewa akwai yankunan da ma'aikatan zaben suka ki zuwa wurin saboda matsalar tsaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani jami'in da ya bukaci a boye sunansa, ya bayyana yankunan da suka ki zuwa da Lilu, Orsumoghu, Ubuluisiuzo, Mbosi da Azia, Daily Trust ta wallafa.

Hakazalika, jami'an NYSC sun zargi cewa wasu 'yan bautar kasa da aka tura wurin domin zaben an maye gurbinsu da wadanda ba 'yan bautar kasa ba.

Jami'in da ya ki bayyana sunansa, ya ce NYSC ta tura jami'ai 1,000 domin zaben Ihiala amma sun fusata ganin cewa da yawansu suna tsaye tare da yawo a sakateriyar.

Jami'an sun jaddada cewa dole ne a tura 'yan bautar kasar da aka horar kuma a biya su.

CP Echeng Echeng, kwamishinan 'yan sandan jihar Anambra ya ce an aike isassun jami'an tsaro domin tabbatar da nasarar zaben a Ihiala.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An tsananta tsaro a Ihiala ta Anambra, sojoji sun hana Sanatan APGA shiga garin

An tsananta tsaro a Ihiala ta Anambra, sojoji sun hana Sanatan APGA shiga garin

A wani labari na daban, tsaro ya tsananta a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra inda ake karasa zaben jihar Anambra a yau Talata, Daily Trust ta wallafa.

Sojoji sun hana Sanata Victor Umeh, wakilin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a jihar daga shiga karamar hukumar Ihiala yayin da aka tura jami'an INEC.

A tare da wasu magoya bayansa da hadimansa, Umeh, wanda ya kwana a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ke Awka yayin da ake tattara sakamakon kananan hukumomi 21 na jihar, an wartake sa daga shiga garin Ihiala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel