Zaben Anambra: Ni fa ban yarda na fadi zabe ba, zamu hadu a kotu - Andy Uba na APC

Zaben Anambra: Ni fa ban yarda na fadi zabe ba, zamu hadu a kotu - Andy Uba na APC

  • Dan takaran jam'iyyar All Progressives Congress APC ya bayyana cewa bai yarda da sakamakon zaben jihar da INEC ta sanar ba
  • Andy Uba yace ta yaya zai fadi a zabe a gundumomin da shugabannin APGA suka koma APC ana saura mako daya zabe.
  • Dan takaran jam'iyyar APC ne ya zo na uku a zaben gwamnan jihar Anambra bisa sanarwar hukumar INEC

Awka - Dan takaran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamnan Anambra da aka kammala, Andy Uba, yace sam ba yarda da sakamakon zaben da INEC ta sanar ba.

A cewarsa, ta yaya zai fadi a zabe a gundumomin da shugabannin APGA suka koma APC ana saura mako daya zabe.

Andy Uba ya bayyana haka ne ranar Asabar yayinda jawabi ga mambobin jam'iyyar APC, rahoton DailyTrust.

Kara karanta wannan

Kada ku saurari abinda PDP ke fadi, so suke kawai su bata min suna: Ali Modu Sherrif ga Gwamnonin APC

Ya lashi takobin cewa zai kai kara kotun zabe.

A cewar Uba,

"Ina da tabbacin APC za ta kwace hakkinta a kotu. Ba yunwa nike ba, kuma babu wanda ya rasa abinci a nan, amma da ikon Allah zamu kwato hakkinmu a kotu."

Ya yi kira da mambobin jam'iyya su kwantar da hankulansu, saboda shi idan ya fara yaki ba ya waiwaye.

Hakazalika Andy Uba ya yi Alla-wadai da jigogin jam'iyyar APC da suka munafurci APC a ranar zabe.

Abokin tafiyarsa a zaben, Barr.Emeka Okafor, ya lashi takobin cewa ba zasu yarda da wannan sakamako ba.

A cewarsa, INEC bata fara zabe a rumfar zabensa ba sai karfe 3 kuma karfe 4 aka rufe.

Andy Iba na APC
Zaben Anambra: Ni fa ban yarda na fadi zabe ba, zamu hadu a kotu - Andy Iba na APC
Asali: UGC

Ba zamu yarda da wannan zaben ba, kawai magudi akayi: APC a zaben Anambra

Kara karanta wannan

Duk da inkarin APC, INEC za ta ba Soludo takardar shaidar lashe zaben Anambra

Kwamitin yakin zaben Sanata Andy Uba ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar Anambra da hukumar zabe ta kasa watau INEC ta sanar ranar Laraba.

Kwamitin tace babu abinda ya faru a zaben nan illa magudi da rufa-rufa kuma ba haka al'ummar jihar suka so ba.

Ambassador Jerry Ugokwe, a jawabin da ya saki ranar Alhamis a madadin kwamitin ya bayyana cewa Hukumar INEC ta yiwa dan takaran APC, Sanata Andy Uba, murdiya ne kawai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel