Tuna baya: Yadda aka kusa halaka zababben gwamnan Anambra saura wata 8 zabe

Tuna baya: Yadda aka kusa halaka zababben gwamnan Anambra saura wata 8 zabe

  • Ana sauran wata 8 ya zama zababben gwamnan Anambra, 'yan bindiga sun kai wa Farfesa Charles Soludo farmaki inda suka nemi rayuwarsa
  • Mummunan lamarin ya faru ne yayin da ya ke ganawa da sama da matasa dubu a Isoufia inda 'yan sanda 3 suka rasu kuma aka sace kwamishinan jihar
  • Daga bisani an sako kwamishinan kuma Soludo ya sha alwashin yi wa 'yan sandan addu'a tare da tallafawa iyalan mamatan

Anambra - Watanni takwas kafin zaben ranar 6 ga watan Nuwamba na gwamnan jihar Anambra, dan takarar jam'iyya mai mulki kuma zababben gwamnan jihar a yanzu, Charles Chukwuma Soludo ya tsallake rijiya da baya, Daily Trust ta wallafa.

An kai wa tsohon shugaban babban bankin Najeriya farmaki a garinsu na Isuofia da ke karamar hukumar Aguata ta jihar yayin da yake tattaunawa da matasan yankin a ranar 31 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun kashe wani kyaftin din soji mai ritaya

Tuna baya: Yadda aka kusa halaka zababben gwamnan Anambra saura wata 8 zabe
Tuna baya: Yadda aka kusa halaka zababben gwamnan Anambra saura wata 8 zabe. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Uku daga cikin jami'an 'yan sandan da ke tsare lafiyarsa sun sheka lahira yayin da 'yan bindigan suka sace kwamishinan jihar, Emeka Ezenwanne inda daga bisani suka sako shi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a yayin jawabi bayan aukuwar lamarin, Soludo ya ce:

"Mun tattauna da matasa kuma mun kammala wurin karfe hudu na yammaci. Muna tsaka da tattaunawa da matasan Isuofia, asalin garinmu ne lamarin ya faru.
"Ni yaron kauye ne kuma a nan ne nake samun kwanciyar hankali. Ina yawata tituna, ina yin doguwar tafiya a kauyenmu saboda nan ne tushe na.
"A yayin da muke tattaunawa, akwai matasa sama da dubu da ke zaune kuma na kammala magana kenan zan basu damar yin tambayoyinsu yayin da dattawan yanki, kwamishinoni da 'yan majalisa ke zaune.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Jami'an tsaro da 'yan IPOB sun shafe sa'o'i uku suna musayar wuta

"Kwatsam muka ji harbin bindiga. Da farko mun yi tsammanin 'yan sanda ne ke harbin iska amma sai muka ji mutane na ihu, lamarin da yasa muka nemi maboya.
"An yi wurin minti goma zuwa sha biyar ana musayar wuta. Bayan mun dawo ne muka ga gawawwaki 3 kwance cikin jini. Muna fatan Ubangiji ya gafarta musu. Za mu cigaba da addu'a tare da tallafawa iyalansu."

Daga ƙarshe, INEC ta ayyana wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambra

A wani labari na daban, hukumar Zabe mai zaman kanta INEC ta ayyana dan takarar jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) Prof Charles Soludo a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan jihar Anambra.

Shugaban Jami'ar Calabar, (UNICAL), kuma baturen zaben na Anambra, ya sanar da cewa Soludo ne zabeben gwamna misalin karfe 1.51 kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Tsohon gwamnan babban bankin na Nigeria ya zamu jimillar kuri'u 112,229 hakan ya bashi damar zama zakara.

Kara karanta wannan

Sokoto: 'Yan ta'adda sun naɗa sabbin hakimai da dagatai, sun bude kasuwanni da gwamnati ta rufe

Asali: Legit.ng

Online view pixel