Babbar magana: APC ta yi waje da jigonta saboda ya taya APGA murnar lashe zabe a Anambra

Babbar magana: APC ta yi waje da jigonta saboda ya taya APGA murnar lashe zabe a Anambra

  • Kusan wata guda da shan kayenta a zaben gwamnan Anambra da aka kammala, tuni jam'iyyar APC a jihar ta fara nuna rashin hadin kai a cikinta
  • Hukumomin APC sun kori wani jigo a jam'iyyar a jihar Anambra kwanaki kadan bayan sanar da cewa Soludo dan takarar APGA ne ya lashe zabe
  • Jigon, Okelo Madukaife, ya yi watsi da rahoton korar da aka yi masa, inda ya bayyana babu shakka cewa har yanzu shi cikakken dan jam'iyyar APC ne

Awka, Anambra - Jam’iyyar APC reshen jihar Anambra ta kori sakataren yada labaranta Okelo Madukaife saboda taya zababben gwamnan Anambra, Farfesa Chukwuma Charles Soludo murnar lashe zabe.

Shugaban jam’iyyar na jihar, Basil Ejidike ne ya sanar da korar Madukaife a wani taron manema labarai a Awka, babban birnin jihar Anambra a ranar Lahadi, 14 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Babban darasin da APC ta koya a zaben Gwamnan Anambra inji Tsohon Hadimin Buhari

Babbar magana: APC ta yi waje da jigonta saboda ya taya APGA murnar lashe zabe a Anambra
APC ta kori jigointa | Hoto: thecable.ng
Asali: Facebook

Ya ce Madukaife da aka dakatar a watan Yunin wannan shekara ya ci gaba da bayyana kansa a matsayin sakataren yada labaran APC har ya zuwa yanzu, ya kuma bayyana a gidan talabijin na kasa don taya Soludo na jam’iyyar APGA murnar lashe zabe.

A cewarsa:

“An dakatar da Okelo ne a watan Yunin bana. Mun yi mamakin yadda ya ci gaba da nuna kansa a matsayin sakataren yada labarai na jam’iyyar. Bai kamata hakan ya kasance ba.
“A madadin jam’iyyar APC ta jihar Anambra, muna so mu bayyana karara cewa Okelo Madukaife ba dan jam’iyyarmu ba ne don haka ba zai iya zama ko aiki a matsayin sakataren yada labarai na jam’iyyarmu a jihar ba.
“Duk wanda ke mu’amala da shi a matsayin dan jam’iyyar APC ko sakataren yada labaran jam’iyyar yana yin hakan ne a karan kansa.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Anambra: Obiano ya yiwa matar da ta ki siyar da kuri’arta kyautar miliyan N1

“Muna so mu bayyana karara cewa dangane da zaben gwamnan Anambra, ba mu taya kowa murna ba.
“Amma muna sane da cewa tun watan Yuni yake ta zage-zage a jam’iyyarmu. An maye gurbinsa da mataimakin sakataren yada labarai, Nonso Chinwuba.”

Da aka tuntube shi ta wayar tarho, Madukaife ya ce har yanzu shi ne sakataren yada labarai na jihar.

A kalamansa:

“Yayin da nake magana da ku, har yanzu ina gudanar da aikina yadda ya kamata, tare da gudanar da ayyukana a matsayina na sakataren yada labarai na jam’iyyar a jihar. Don haka, ban san abin da kuke magana akai ba."

Babban darasin da APC ta koya a zaben Gwamnan Anambra inji Tsohon Hadimin Buhari

A wani labarin, tsohon mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar majalisa, Abdulrahman Kawu Sumaila, ya tofa albarkacin bakinsa game da zaben Anambra.

Honarabul Abdulrahman Kawu Sumaila ya yi jawabi a shafin Facebook a karshen makon da ya wuce, yana kira ga APC ta dauki darasi a zaben gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamnan PDP ya amince da shan kaye, ya taya Soludo murna

Abdulrahman Kawu Sumaila wanda ya tabar wakiltar Takai da Sumaila a majalisar tarayya yace an wuce lokacin da za a rika kakaba ‘yan takara da karfi da yaji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel