Zaben jihohi
Mun kawo jerin Gwamnonin Jihohin da sai sun yi da gaske za su koma mulki a Najeriya. A cikinsu akwai Gwamna Bala Mohammed da Umaru Fintiri a Arewa maso gabas.
Bello Kirfi ya yi magana kan tunbuke shi daga kan kujerar Wazirin Bauchi. Tun da aka tube masa sarauta, Dattijon ya yi alkawarin Gwamnan Bauchi ba zai zarce ba
Aishatu Binani, 'yar takarar kujerar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam'iyyar APC, ta kai wa shugaba Buhari ziyara hara fadarsa da ke Aso Villa a Abujaa.
Fatima Abubakar, 'yar takarar kujerar gwamnan jihar Borno karkashin jam'iyyar ADC ta bayyana cewa a shirye take don lallasa Gwamna Zulum a zabe mai gabatowa.
Kotun sauraron kararrakin zabe dake zama a Ekiti ta jaddada nasarar Oyebanji a zaben Gwamnan jihar da aka yi a watan Yunin 2022. Kotun ta kori karar Segun Oni.
Ganin zaben 2023 ya karaso, an ji labari shugaban Kungiyar Abia Christian Community (ACC) za ta fadawa mabiyanta ‘yan takaran da za a zaba a kowace kujerar 2023
Ejike Agbo ya yi karar APC da ‘dan majalisar Ohaukwu ta Kudu, Hon. Chinedu Onah a kan rashin nasarar da ya samu wajen neman tikitin takara a APC a zaben 2023.
Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hare-hare da ake kai masu da kuma sayen kuri’u za su iya kawo barazana a zaben 2023 da hukumar za ta shirya.
Mata sun daura damarar ganin ba a barsu a baya ba. Yanzu haka kimanin mata 24 ne aka tsayar takarar matakin gwamna a jam'iyyun siyasa daban-daban a fadin kasar.
Zaben jihohi
Samu kari