Jigo a PDP Ya Ankarar da Jama’a, Ya Ce Ana Yunkurin Hallaka ‘Dan Takarar Gwamna

Jigo a PDP Ya Ankarar da Jama’a, Ya Ce Ana Yunkurin Hallaka ‘Dan Takarar Gwamna

  • Bode George wanda jagora ne a jam’iyyar PDP a Kudancin Najeriya, yana tare da Gbadebo Rhodes-Vivour
  • ‘Dan siyasar ya kira taro na musamman, ya shaidawa mutanen Legas ana shirin kashe ‘Dan takaran LP
  • Cif George ya ce da zarar wani abin ya faru da Gbadebo Rhodes-Vivour, an san su wanene suka aikata

Lagos - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP, Bode George, yana ikirarin akwai mummunan shirin da ake yi na kashe Gbadebo Rhodes-Vivour.

The Cable ta rahoto Cif Bode George yana cewa idan wani abin ya faru da Gbadebo Rhodes-Vivour, mutanen Najeriya sun san wanda za su kama da laifi.

Da ya kira wani taron manema labarai a ranar Litinin, Bode George ya ce masu rike da Legas sun nufi hallaka ‘dan takaran LP kafin ranar zaben Gwamna.

Kara karanta wannan

Mako 1 da Zabe, Gwamnan PDP Ya Fadi Abin da Ya sa Atiku Ya Rasa Kujerar Shugaban Kasa

Jawabin Cif Bode George

Mu na so mu sanar da mutanen Najeriya game da wani mugun nufi na hallaka ‘dan takarar Gwamna na jam’iyyar LP, Gbadebo Rhodes-Vivour.
Masu rike da Legas sun zo da sabon shiri, su na so su batar da shi kafin lokacin zaben ranar Asabar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mu na jan-kunne, idan wani abin ya faru da wannan mutum ‘Dan ainihin Legas da kaddara ta tsara zai karbe jiharmu daga hannun mugaye, a san wa za a kama.

- Bode George

Gbadebo Rhodes-Vivour
Gbadebo Rhodes-Vivour yana kamfe Hoto: @GRVlagos
Asali: Twitter

George ya ce a zabi jam’iyyar LP

Sahara Reporters ta rahoto George yana mai yin kira ga mutanen jihar Legas suyi watsi da siyasar raba kan al’umma, su zabi jam’iyyar LP a ranar Asabar.

Da alama ‘dan siyasar yana cikin jiga-jigan PDP da suka goyi bayan Peter Obi na LP a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Ainihin Dalilan da Suka Jawo APC Ta Ji Kunya a Legas, Kaduna, Katsina da Jihohi 9

A jawabin da yayi jiya, tsohon Gwamnan ya bukaci hukumar INEC ta tabbatar an yi amfani da na’urorin BVAS a wajen aika sakamakon zabe daga rumfuna.

George ya bada shawara bai kamata a dauki lokaci ba tare da an aika sakamakon zabuka ba, yana tsoron cewa za a iya yin magudi muddin aka yi sake.

Mista Gbadebo Rhodes-Vivour shi ne ya tsaya takarar Gwamnan jihar Legas a karkashin jam’iyyar LP, ana tunanin zai iya kawowa tazarcen APC cikas.

Shari'ar karar zaben 2023

Atiku Abubakar da Peter Obi su na kalubalantar nasarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaben bana, kuma sun shigar da kara a kotun sauraron korafin zabe.

An ji labari tsohon AGF, Akin Olujimi da Muiz Banire da tsohon Gwamnan jihar Bauchi sun yarda su shiga cikin Lauyoyin zababben shugaban Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel