Da Walakin: Dalilin INEC na Cire Sunan Alhassan Doguwa Daga Zababbun ‘Yan Majalisa

Da Walakin: Dalilin INEC na Cire Sunan Alhassan Doguwa Daga Zababbun ‘Yan Majalisa

  • Baturen zaben Tudun Wada da Doguwa ya jawo aka soke nasarar Hon. Alhassan Ado Doguwa a APC
  • Ibrahim Adamu Yakasai ya sanar da Hukumar INEC cewa tursasa shi aka yi wajen sanar da sakamako
  • Jam’iyyar NNPP ta yi amfani da ikirarin Farfesan, ta yi nasara aka dakatar da nasarar da aka ba APC

Kano - Bayanai sun fito a game da dalilin da ya sababba hukumar zabe watau INEC ta soke nasarar Alhassan Ado Doguwa a zaben majalisar tarayya.

A wani rahoto da ya zo a Daily Nigerian, an fahimci abin da ya sa har yanzu ba tsaida asalin wanda zai wakilci Tudun Wada da Doguwa a majalisa ba.

Uzurin da hukumar ta bada a sakamakon zaben da aka shirya a ranar 25 ga watan Fubrairun shi ne an sanar da sakamamakon ne ta matsin lamba.

Kara karanta wannan

"Ba Mu Ji Dadi Ba": Kwankwaso Ya Fusata, Ya Yi Allah Wadai Da Belin Ado Doguwa

Abin da hakan yake nufi shi ne akwai yiwuwar an yi magudi wajen ayyana wanda ya yi nasara.

Karfi da yaji aka yi wa Farfesa

Rahoton ya ce Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai ya rubutawa Babban kwamishinan zabe na Kano takarda, ya sanar da shi hakikanin abin da ya faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai ya fadawa Abdu Zango cewa karfi da yaji aka yi masa har ya ba Honarabul Alhassan Doguwa nasara a zaben.

Alhassan Ado Doguwa
Alhassan Ado Doguwa a Majalisa Hoto : premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wasikar ta ce Farfesan ya ayyana ‘dan takaran APC a matsayin wanda ya yi galaba ne saboda an yi wa rayuwarsa da sauran ma’aikatan zabe barazana.

Saboda gudun a ga bayansa, masanin ya ce Alhassan Doguwa ya yi galaba a kan Salisu Yusha’u 'Soja' wanda ya yi takara a jam’iyyar adawa ta NNPP.

'Yan daba sun bada wa'adin sa'a guda

Kara karanta wannan

Wani Soja Ya Bindige Oga, Ya Harbe Abokin Aikinsa, Sannan Ya Kashe Kan Shi

Baya ga haka, malamin jami’ar ya ce ‘yan daba sun zagaye ofishin INEC, sun nuna za su kona wurin idan bai sanar da sakamakon a cikin sa’a guda ba.

Wannan wasika ce NNPP tayi amfani da ita, ta aikawa shugaban hukumar INEC wajen ganin an dakatar da nasarar jam’iyyar APC domin ayi bincike.

"Yakasai mutumin kirki ne"

Abu Sufyan Fahruddin yana cikin daliban Farfesa Yakasai a Jami’ar ABU Zariya, ya shaida mana malamin mutum ne mai saukin kai da dadin mu’amala.

Matashin yake cewa a duk inda mutum ya ci karo da malamin, zai iya ba shi shawara a kan harkar karatu da rayuwa, tamkar uba yake wajen dalibai.

Abdul Jalil Enesi ya yi karatu a wajen malamin, ya bayyana shi a matsayin mutum mai son jama’a, faram-faram, kyauta, da wasa da dalibai da bin ka’ida.

Baya ga kasancewarsa uba na kungiyoyin ‘yan makaranta, surukuntaka ta hada shi da wani dalibinsa.

Kara karanta wannan

‘Dan Shekara 27 Daga Arewa Ya Ajiye Tarihin Zama ‘Dan Autan ‘Yan Majalisar Tarayya

Asali: Legit.ng

Online view pixel