Zaɓen Gwamnoni: Jam'iyyar Labour Party Ta Nemi Mambobinta Da Su Zaɓi Ƴan Taƙarar Jam'iyyar Kaɗai

Zaɓen Gwamnoni: Jam'iyyar Labour Party Ta Nemi Mambobinta Da Su Zaɓi Ƴan Taƙarar Jam'iyyar Kaɗai

  • Ana dab da a fara zaɓen gwamna, jam'iyyar Labour Party, ta fito tayi wani muhimmin kira ga mambobin ta.
  • Jam'iyyar ta nemi mambobin ta da magoya bayan ta da su tabbatar ƴan takarar jam'iyyar kawai suka zaɓa a zaɓen ranar Asabar
  • Jam'iyyar ta kuma musanta jita-jitar cewa tayi haɗaka da wasu jam'iyyun a zaɓen da za a fafata na ranar Asabar

Abuja- Shugaban jam'iyyar Labour Party (LP) na ƙasa, Julious Abure, ya nemi mambobi da magoya bayan jam'iyyar da su tabbatar sun zaɓi ƴan takarar dake yin takarar a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar a zaɓen gwamnoni na ranar Asabar.

Abure yayi wannan kiran ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, a birnin tarayya Abuja. Rahoton Vanguard.

Peter
Dan Takarar Jam'iyyar Labour Party Hoto: Peter
Asali: UGC

Yayi bayanin cewa a yayin shirye-shirye suka kusa kammaluwa kan zaɓen na ranar Asabar, jam'iyyar na yin duk mai yiwuwa wajen ganin cewa ƴan takarar sun yi nasara a ranar zaɓe, ba wai takara kawai suka yi ba. Rahoton NewsWire

Kara karanta wannan

An Dakatar da Shugaban Jam'iyyar APC a Neja Bisa Zargin Dangwalawa Atiku Kuri'a

A kalamansa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Wannan kiran ya zama wajibi duba da rahotannin da muke samu na wasu ƴan siyasa daga wasu jam'iyyun masu iƙirarin cewa sun cimma yarjejeniya da Obidients da magoya bayan LP, domin su kaɗa musu ƙuri'a a zaɓen ranar Asabar.
Muna son mu sanar da cewa sakatariyar uwar jam'iyya ta LP, bata bayar da wani umurni ba ga sauran rassan jam'iyyar domin su yi haɗaka ko marawa wani ɗan takara baya, face ƴan takarar LP a zaɓen ranar Asabar.
"Mambobin mu ba wai kawai za su fito su kaɗa ƙuri'un su bane, amma za su tabbatar sun sanya ido kan zaɓen kamar yadda doka ta tanada."
“Jam'iyyar LP bata yi wata haɗaka da kowace jam'iyya ba kafin zuwan zaɓen ranar Asabar."

Tinubu Ba Shugaban Ƙasar Da Muka Zaɓa Bane", Wata Babbar Fasto

Kara karanta wannan

Abin Ban Takaici Cocin Gidan Gwamnati Ta Aso Rock Za'a Rufe ta Na Tsawon Shekara 4 - Okowa

A wani labarin na daban kuma, wata babbar fasto tace Tinubu ba shi bane zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ta.

Bola Tinubu na jam'iyyar APC shine zaɓaɓɓen shugaban ƙasan Najeriya, kamar yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana

Asali: Legit.ng

Online view pixel