Hukumar Zabe Ta INEC Ta Fara Rarraba Kayan Aikin Zaben Gwamna a Jihar Kaduna

Hukumar Zabe Ta INEC Ta Fara Rarraba Kayan Aikin Zaben Gwamna a Jihar Kaduna

  • Tuni hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta fara rarraba kayan aikin zabe a jihar Kaduna da ke Arewa
  • Za a yi zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha a fadin kasar nan a ranar Asabar, 11 ga watan Maris mai zuwa
  • An yi zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya samu nasarar lashewa da kuri’un da suka fi na Atiku da Peter Obi

Jihar Kaduna - Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya (INEC) ta fara rarraba kayayyakin da za a yi amfani dasu a zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jiha na ranar Asabar.

Hakazalika, hukumar ta fara raba ma’aikatan da za su tsaya tsayin daka a wannan aiki na zabe a jihar Kaduna da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, BBC ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Matsala ta faru: Jerin mazabun sanata 8 da dole za a sake zabe, INEC ta fadi yaushe

A cewar INEC, ya zama dole ta fara wannan shirin tun ranar Laraba don saukakawa da samun damar shirya komai cikin tsanaki da wuri.

Kayan aikin zaben da INEC ke rabawa a Kaduna
Kayan aikin zabe ya fara rabuwa a jihar Kaduna | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Hakazalika, ta ce hakan ne zai rage aukuwar matsalolin da kuma gano abubuwan da ya kamata a gyara gabanin zaben mai zuwa a ranar Asabar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tuni dai INEC ta fara tura muhimman kayan aikin zaben zuwa Babban Bankin CBN, kana za a raba su zuwa kananan hukumomi 23 na jihar.

Za a yi zabe a Najeriya ranar 11 ga wata

Idan baku manta ba, rahotanni sun bayyana yadda hukumar zabe ta INEC ta tsara gudanar aikin zabe a wasu daga jihohin kasar a ranar 11 ga watan Maris

Wannan zabe zai zama na gwamnoni da ‘yan majalisun dokokin jiha bayan da aka kammala na shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar 25 ga watan Faburairu.

Kara karanta wannan

“Duk Bayanan Kan BVAS Na Nan Daidai”: INEC Ta Ba Yan Najeriya Da Kotu Tabbaci

An gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya, inda Bola Ahmad Tinubu ya lashe zabe da kuri’u sama da miliyan 8, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

El-Rufai ya taya Tinubu murnar lashe zabe

A wani labarin kuma, kun ji yadda gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya taya Bola Ahmad Tinubu murnar lashe zaben shugaban kasa a bana.

El-Rufai ya bayyana cewa, yana da yakinin Tinubu zai ba ‘yan Najeriya abin da suke bukata tunda suka bashi kuri’unsu a wannan karon.

Hakazalika, ya ce Tinubu cikakken dan Najeriya mai gogewa a shugabanci, don haka babu abin damuwa kan yadda zai ciyar da kasar nan gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel