Jam'iyyar NNPP Ta Haramta Yin Haɗaka Da Wasu Jam'iyyun Ga Shugabannin Ta Da Mambobin Ta

Jam'iyyar NNPP Ta Haramta Yin Haɗaka Da Wasu Jam'iyyun Ga Shugabannin Ta Da Mambobin Ta

  • Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta bayyana cewa bata da shirin yin haɗaka da kowace jam'iyya
  • Jam'iyyar ta kuma gargaɗi jagororinta da mambobin ta kan su guji yin wata tattaunawa da niyyar yin haɗaka da kowace jam'iyya
  • Jam'iyyar ta NNPP ta sanar da hukuncin da ta tanada ga duk wanda ya saɓa wannan umurnin na ta

Abuja- Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), ta gargaɗi mambobin ta, shugabanni da ƴan takara kan yin haɗaka da kowace jam'iyya domin yin nasara a zaɓen gwamna da na ƴan majalisun jiha dake tafe.

Jam'iyyar tayi wannan gargaɗin ne a cikin wata sanarwa da sakataren ta na ƙasa, Mr Agbo Major, ya fitar a ranar Lahadi, a birnin tarayya Abuja. Rahoton Vanguard

Jam'iyyar NNPP
Jam'iyyar NNPP Ta Haramta Yin Haɗaka Da Wasu Jam'iyyun Ga Shugabannin Ta Da Mambobin Ta Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

Major ya shawarci mambobin jam'iyyar da su mayar da hankali, su yi kamfen ba kama hannun yaro domin tabbatar da cewa sun samu gagarumar nasara a zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisun jihohi a faɗin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zabe: Tsoffin Gwamnoni da Ministoci, Sanatoci da Wasu Manya Sun Huro Wa INEC Wuta Kan Abu 1

A kalamansa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Jam'iyyar mu bata wata tattaunawa domin yin haɗaka da wata jam'iyya a cikin zaɓukan nan."
"Haka kuma, shugabannin jam'iyya, mambobi, da ƴan takara a kowane mataki ba su da hurumin tattaunawa ko yin kowace irin haɗaka da wata jam'iyya domin lashe zaɓene gwamnoni da na ƴan majalisun jiha dake tafe.
"Duk wanda ya marawa wani ɗan takara na wata jam'iyya zai fuskanci hukunci daidai da kundin tsarin mulkin NNPP, wanda ya kama daga dakatarwa daga aiki, dakatarwa daga jam'iyya sannan da yiwuwar kora."

Major ya bayyana cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta yiwa jam'iyyar NNPP, rajista a shekarar 2002, sannan tun daga wannan lokacin ta cigaba da faɗaɗa harkokin siyasar ta a zaɓukan ƙasar nan. Rahoton The Cable

Ya kuma bayyana cewa jam'iyyar tayi kataɓus wanda ya wuce mataki na huɗu da INEC ta bata a sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.

Kara karanta wannan

An Dakatar da Shugaban Jam'iyyar APC a Neja Bisa Zargin Dangwalawa Atiku Kuri'a

Tsohon Ministan Buhari da Tsohon Gwamna Su na Hangen Shugabancin Majalisar Dattawa

A wani labarin na daban kuma, wasu ƴan siyasa sun fara hangen shugabancin majalisar dattawan Najeriya ta goma.

Daga cikin masu wannan hangen dai akwai tsohon ministan Buhari da kuma wani tsohon gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel