Zaɓen Gwamnoni: Abdullahi Adamu Ya Sa Labule Da Gwamnonin APC a Abuja

Zaɓen Gwamnoni: Abdullahi Adamu Ya Sa Labule Da Gwamnonin APC a Abuja

  • Ana dab da a fara zaɓen gwamnoni a Najeriya, shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ya sa labule da gwamnonin APC
  • Shugaban jam'iyyar yana ganawa ne dai da gwamnonin a hedikwatar jam'iyyar ta ƙasa da ke a birnin tarayya Abuja
  • Jam'iyyar tana ƙalubale sosai a gabanta a zaɓen gwamnoni duba da yadda ba tayi nasara ba a wasu jihohin da take mulki a zaɓen shugaban ƙasa

Abuja- Gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), sun sanya labule da shugaban jam'iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, a yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar dokokin jiha.

A ranar Asabar 11 ga watan Maris ne dai za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar dokokin jihohi a tarayyar Najeriya.

Adamu
Zaɓen Gwamnoni: Abdullahi Adamu Ya Sa Labule Da Gwamnonin APC a Abuja Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ana gudanar da taron ne tsakanin Adamu da gwamnonin a hedikwatar jam'iyyar ta ƙasa dake birnin tarayya Abuja.

Bayan shugaban jam'iyyar, akwai mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar waɗanda suka halarci taron.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yawa daga cikin gwamnonin jam'iyyar APC suna neman tazarce a zaɓen ranar Asabar.

Gwamnoni irin su Babagana Zulum na Jihar Borno, Inuwa Yahaya na jihar Gombe, Bello Matawalle na jihar Zamfara, Babajide Sanwo Olu na jihar Legas, Dapo Abiodun na jihar Ogun

Da kuma Hope Uzodinma na jihar Imo, na neman komawa kan kujerar su karo na biyu.

Jam'iyyun adawa sun fara ganin cinta a jihohin da APC ke mulki a zaɓen ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, na shugaban ƙasa da na ƴan majalisun tarayya.

Jihohi irin su Legas, Kano, Kaduna, Katsina, Nasarawa, da Plateau, duk sun faɗa hannun ƴan adawa a zaɓen duk kuwa da cewa suna a ƙarƙashin mulkin jam'iyyar APC.

Jam'iyyar APC Ta Nada Manyan Lauyoyi 12 Da Zasu Kare Nasarar Tinubu a Kotu

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar APC ta naɗa wasu manyan lauyoyi waɗanda zasu kare nasarar Tinubu a kotu.

Ƴan takarar da suka sha kashi dai a zaɓen shugaban ƙasa sun garzaya kotu domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel