Kudin Kamfe: ‘Yan PDP Sun Kai ‘Dan Takarar Gwamna Kotu a Kan Naira Biliyan 1.05

Kudin Kamfe: ‘Yan PDP Sun Kai ‘Dan Takarar Gwamna Kotu a Kan Naira Biliyan 1.05

  • Za ayi shari’a tsakanin bangaren su Yakubu Lado Danmarke da mutanen Lawal Uli a Jam’iyyar PDP
  • Uli da ‘yan majalisarsa sun yi karar Sanata Danmarke, Aminu Yar’dua, da Mustapha Inuwa a kotun Katsina
  • Idan an tsaida lokacin shari’a, za a ji inda ‘Yan takara suka kai kudin yakin neman zaben PDP na jihar

Katsina - Kwanaki kadan suka rage a shirya zaben Gwamnoni da ‘yan majalisun dokoki, sai aka ji jam’iyyar PDP ta shigar da karar ‘dan takararta.

Rikicin cikin gidan PDP a Katsina ya fito karara a halin yanzu, Daily Trust ta ce wasu ‘ya ‘yan jam’iyya sun yi karar Sanata Yakubu Lado Danmarke a kotu.

Baya ga ‘dan takarar Gwamnan, wadanda suka shigar da karar sun hada da mai neman mataimakin Gwamna a PDP a 2023, Aminu Ahmed Yar’dua.

Kara karanta wannan

Aiki ya kwabe: Cikin kowa ya duri ruwa, jiga-jigan PDP 10,000 sun koma APC a jihar Arewa

Sauran wadanda aka yi kara sun hada da shugaban tsagin Danmarke a PDP, Lawal Danbaci da shugaban yakin zabe, Mustapha Muhammad Inuwa.

Kudin kamfe sun yi kafa

Mustapha Muhammad Inuwa shi ne yake jagorancin kwamitin yakin neman takarar Atiku/Lado, a 2022 ya bar mukaminsa na sakataren gwamnatin jiha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shigar da karar mutum fiye da goma a babban kotun jihar Katsina ne a game da wasu kudi Naira Biliyan 1.05 na yin zirga-zirgar yakin neman zabe.

Yakubu Lado Danmarke
Yakubu Lado Danmarke yana kamfe a Kankara Hoto: @SenLadoDanmarke
Asali: Twitter

Jaridar ta samu takardar karar mai lamba KTH/337/23, inda aka fahimci shugaban rikon kwarya na PDP da wasu ‘yan majalisarsa suka shigar da karar.

Lawal Uli da shugabanni 13 suka maka bangarensu Sanata Danmarke a madadin PDP ta Katsina.

Sai abin da kotu ta zartar

Masu karar su na so wadanda ake tuhuma su yi cikakken bayanin inda aka kai N1,050,000,000 da aka ware domin yakin neman zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Ƙara Rikita Lissafin APC Ana Dab da Zaben Gwamnoni a Najeriya

Lauyoyin Lawal Uli sun bar wa kotun jihar wuka da nama ta dauki matakin da ya dace.

Takardar shigar da karar ta isa kotu a farkon makon nan, amma har zuwa yammacin Talata ba a samu labarin cewa an tsaida ranar da za a soma zama ba.

Zaben Tudun Wada/Doguwa

A makon nan aka samu rahoto malamin zabe ya tona asirin komai daga baya, wanda hakan ya jawo tazarcen Hon. Alhassan Ado Doguwa ya shiga rububi,

Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai ya ce an yi wa rayuwarsu barazana, saboda haka aka tilasta shi ya sanar da sakamakon zaben Tudun Wada/Doguwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel