Labaran garkuwa da mutane
Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi awon gaba da Dagaci, ɗan gidan sarauta da wani mutum ɗaya a kauyen Ketti da ke birnin tarayya Abuja, sun nemi kuɗin fansa.
Wasu tsagerun yan bindiga da ake zaton masu sace mutane ne sun yi garkuwa da shahararen mai wa'azin nan na gidan talbijin, Rabaran Mike Ochigbo a jihar Adamawa.
'Yan sanda a jihar Nasarawa sun yi nasarar kama masu garkuwa da mutane su 26 tare da kubutar da mutane biyu da masu garkuwar suka sace. Jami'in hulda da jama'a.
Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da ma'aikata akalla biyu na hukumar sufurin jiragen kasa (NRC) da ke aiki a tashar Agbor, jihar Delta, sun kira waya.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi ajalin abokin aikinsu yayin da suka yi kokarin harbe wani matashi a kauyen Yarimawa da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano.
Hukumar jami'ar jihar Filato ta tabbatar da labarin harin da 'yan bindiga suka kaai gidan kwanan ɗalibai mata a jami'ar jihar Filato, amma ba su samu nasara ba.
A karshen makon jiya wasu daga cikin daliban makarantar FGC Yauri da aka yi garkuwa da su, sun kubuta. Iyaye sun dauki kwanaki su na sasantawa da 'yan bindiga.
Wasu tsagerun 'yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban karamar hukumar a jihar Taraba, inda suka hallaka dan sandan da ke bashi kariya a lokacin da suke hanya.
Gwarazan jami'an hukumar sojin Najeriya sun samu nasarar kubutar biyu daga cikin ma'aikatan ƙungiyar NGO uku da yan ta'adda suka yi garkuwa da su a jihar Borno.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari