Masu Garkuwa da Kwamishina a Kuros Riba Sun Nemi Fansar Miliyan N150m

Masu Garkuwa da Kwamishina a Kuros Riba Sun Nemi Fansar Miliyan N150m

  • Yan bindigan da suka yi awon gaba da kwamishinar harkokin mata a jihar Kuros Riba sun nemi kuɗin fansa kafin sako ta
  • Rahotanni daga mawallafa na jihar sun nuna cewa masu garkuwan sun nemi a biya su miliyan N150m a matsayin kuɗin fansar matar
  • Idan baku manta ba a ranar 1 ga watan Fabrairun da muke ciki ne aka yi awon gaba da Farfesa Njar a yankin Kalaba ta kudu

Cross River - Bayan shafe kwanaki Takwas, Maharan da suka yi garkuwa da kwamishinar harkokin mata a jihar Kuros Riba, Farfesa Gertrude Njar, sun faɗi kuɗin da suke bukata a matsayin fansa.

Jaridar Punch ta rahoto cewa masu garkuwan sun nemi a tattara masu naira miliyan N150m a matsayin fansar sako kwamishinar.

Gwamna Ben Ayade.
Masu Garkuwa da Kwamishina a Kuros Riba Sun Nemi Fansar Miliyan N150m Hoto: punchng
Asali: UGC

Wannan na kunshe ne a wani rubutu da mai kafar watsa labaran Cross Rivers Watch, Agba Jalingo, ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook.

Kara karanta wannan

Tsawaita kashe tsoffin kudi: Abu 3 da kowa ya kamata ya sani game da hukuncin kotun koli

Kwamishinar ta shiga hannun masu garkuwa da mutanen ne a tsakankanin yankin Avenue-Atamunu, ƙaramar hukumar Kalaba ta kudu da safiyar 1 ga watan Fabrairu, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Kuros Riba ta tabbatar da sace kwamishina

Rahotan News Wire ya bayyana cewa kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kai na Kuros Riba, Eric Anderson, ya tabbatar da lamarin mara daɗin ji ga 'yan jarida.

Ya kuma bayyana cewa tuni aka tuntuɓi rundunar 'yan sanda ta jihar da kuma kwamishinan ayyuka na musamman game da garkuwa da Farfesa Njar.

Bugu da ƙari, ya nuna matuƙar damuwarsa kan, "Yadda Irin wannan ci gaban mara kyau zai faru a cikin tsakiyar gari."

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa kwamishinar mata, Farfesa Njar, tare da wasu kwamishinoni ba su jima ta karban rantsuwar kama aiki ba a gwamnatin gwamna Ben Ayade na Kuros Riba.

Kara karanta wannan

Ana neman matar gwamna: Kotu ta mika dangin Yahaya Bello gidan yari kan badakalar N3bn

'Yan Daban PDP Sun Yi Garkuwa da Dan Takarar Gwamnan APC a Ribas

A wani labarin kuma Wasu tsagerun yan daban siyasa sun tsare mai neman zama gwamnan jihar Ribas a inuwar APC

A wani bidiyo da ya bayyana ta hannun wanda abun ya faru a gabansa, ya nuna yadda yam daban suka bude wuta kan mai uwa da wabi a garin Opobo, inda lamarin ya auku.

Wannan ba shi ne na farko da yan bindigan da ake tsammanin yan daban siyasa ne suke kai hari wurin yakin neman zaɓe ba a jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel