Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugaban PDP da Jagoran Al'umma a Kaduna

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugaban PDP da Jagoran Al'umma a Kaduna

  • Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban jam'iyyar PDP na gunduma a karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna
  • Wani ganau ya bayyana cewa maharan sun saje da jirgin yakin neman zabe da ya shiga kauyen kuma wannan ne karo na farko
  • Bayan ɗan siyasan, yan bindigan sun sace wani shugaban al'umma jim kaɗan bayan sun dawo daga wurin kamfe

Kaduna - Wasu tsagerun 'yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban Peoples Democratic Party (PDP) da shugaban al'umma a ƙaramar hukumar Giwa, jihar Kaduna.

Wani Ganau ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa yan bindigan jejin sun kutsa cikin ƙauyen Ɗan Mahawayi da misalin karfe 11:00 na daren ranar Lahadi kana suka yi gaba da mutanen biyu.

Harin yan bindiga.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugaban PDP da Jagoran Al'umma a Kaduna Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Waɗanda suka faɗa hannun yan ta'addan su ne, Alhaji Bala Alhassan Marafa, shugaban jam'iyyar PDP na gundumar Dan Mahawayi da kuma Suleiman Isiyaku Mai Siga.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Ɗau Zafi: Kwana 4 Gabanin Zabe, Jam'iyyar PDP Ta Kori Ɗan Takarar Gwamna Kan Laifi 1

Wani da abun ya faru a kan idonsa ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Baki ɗayanmu mun ɗauka yan bindiga na daga cikin tawagar kamfen da ta shigo yankin saboda bayan mutanen biyu sun dawo daga wurin taron kamfe ne yan ta'addan suka tasa ƙeyarsu."
"Wannan shi ne karo na farko da aka yi garkuwa da wani a kauyen Ɗan Mahawayi."

Haka nan wani ɗan Banga ya ce lamarin ya faru ne bayan gama ralin kamfen ɗan takarar majalisar tarayya mai wakiltar Giwa da Birnin Gwari, Aminiya ta rahoto.

Mazauna garin Ɗan Mahawayi sun jaddada cewa wannan ne hari na farko da yan bindiga suka kai masu domin suna zuwa biyan bukatunsu amma ba su kai hari

Duk wani yunkuri na jin ta bakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna, ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bam Ya Tashi a Sakatariyar Karamar Hukuma a Arewacin Najeriya

Haka zalika da aka tuntubi jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Kaduna, Muhammaed Jalige, domin jin ta bakinsa ba'a same shi ta wayar tarho ba.

Bam ya tashi a jihar Kogi

A wani labarin kun ji cewa Bam ya tashi a Sakatariyar karamar hukumar Okehi da ke jihar Kogi ranar Litinin

Gwamnatin Kogi tatabbatar da aukuwar lamarin da cewa wani abun fashewa ya tashi a Sakatariyar Okehi, ana zaton bam ne amma bai halaka kowa ba.

A cewar mai baiwa gwamna shawara kan harkokin tsaro, tuni jami'an tsaro suka zagaye wurin domin dawo da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel