Wasu ’Yan Bindiga 3 Sun Mutu a Wani Harin da Suka Kai Ofishin ’Yan Sanda

Wasu ’Yan Bindiga 3 Sun Mutu a Wani Harin da Suka Kai Ofishin ’Yan Sanda

  • Jami'an 'yan sandan jihar Anambra sun yi nasarar hallaka wasu tsagerun 'yan ta'adda a wani kazamin karin da suka kai
  • An ruwaito cewa, tsagerun sun farmaki ofishin 'yan sanda da nufin kone shi, amma musayar wuta ta barke a tsakaninsu
  • An ce an hallaka wasu tsageru uku yayin da 'yan sanda uku suka rasa rayukansu a bakin aiki, ciki har da wani DPO

Jihar Anambra - Wasu tsagerun ‘yan bindiga a ranar Litinin 20 Faburairu, 2023 sun mutu a hannun ‘yan sandan ofishin Awada a kusa da Obosi a jihar Anambra.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa, wadanda aka sheken sun bankawa ofishin ‘yan sandan wuta, amma suka gamu da tsaiko yayin da ‘yan sandan suka yi musu luguden wuta.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, sakataren yada labarai na gwamnan Charles Soluo, Christian Aburime ya fa fada a cikin wata sanarwa cewa, an kwato bindigogi AK-47 guda biyu a hannun ‘yan ta’addan.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: PSC Ta Cire Sunan Tsohuwar Jigon APC Naja'atu Daga Cikin Masu Aikin Zabe

An hallaka 'yan bindiga da 'yan sanda a Anambra
Wasu ’Yan Bindiga 3 Sun Mutu a Wani Harin da Suka Kai Ofishin ’Yan Sanda | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

An kashe DPO da wasu mutane daban

A wani rahoton jaridar Daily Post, an ce 'yan ta'aaddan sun hallaka wani DPO a lokacin da suka kawo mummunan harin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, an hallaka wasu jami'an 'yan sanda uku a harin da ake zargin 'yan ta'addan haramtacciyar kungiyar IPOB ne suka kai.

A bangare guda, wasu mazauna yankin da suka shaida faruwar lamarin sun ce, an kashe DPO ne da kuma jami'ai uku inda aka kashe 'yan ta'addan biyu.

Ya zuwa yanzu dai ba a samu nasarar jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar ba, DSP Tochukwu Ikenga kasancewar wayarsa ba ta shiga, kuma bai dawo da sakon tes da aka tura masa ba.

An harbe jigon APC a lokacin kamfen a jihar Osun

A wani labarin kuma, kunji yadda rikici ya barke aka hallaka wani jigo kuma mamban jam'iyyar APC a jihar Osun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Adamu da Gwamnoni 4 Sun Gana da Ministan Buhari Kan Sauya Naira, Sabbin Bayanai Sun Fito

Kisan Ebenezer Alaro ya tada kura tsakanin jam'iyyar APC da PDP a jihar, inda jam'iyyun biyu ke zargin juna da faruwar kashe-kashe da hare.

Wannan lamari dai na zuwa ne yayin da ya saura kwanaki akalla biyar kafin a yi zaben 2023 na shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel