Mun Siya Makamai da Sabbin Naira, Za Mu Yaki Gwamnati Dasu, Inji Shugaban ’Yan Bindiga Kachalla

Mun Siya Makamai da Sabbin Naira, Za Mu Yaki Gwamnati Dasu, Inji Shugaban ’Yan Bindiga Kachalla

  • Dan ta’addan nan da ke addabar al’ummar Arewa maso Yammacin Najeriya ya bayyana samun sabbin Naira da aka buga
  • A cewarsa, ya samu kudaden da wasu ‘yan Najeriya da yawa basu samu ba tun farkon yawon sabbin kudaden a gari
  • Gwamnatin Najeriya ta yi sauyin kudi domin dakile matsalolin ta’addanci a yankuna daban-daban na kasar nan

Najeriya - Gawurtaccen shugaban ‘yan bindiga, Kachalla Balleri ya ce tawagarsa ta ‘yan ta’adda ta siya sabbin makamai da kudade sabbi da aka buga kwanan nan, Daily Trust ta ruwaito.

Balleri na daya daga cikin ‘yan bindigan da suka addabi yankunan jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna da ma tsagin jamhuriyar Nijar mai makwabtaka da Najeriya.

Shugaban ‘yan ta’addan ya nuna a wani bidiyo cewa, ya mallaki sabbin Naira da ‘yan Najeriya ke ci gaba da shan wahala wajen nemowa a bankuna.

Kara karanta wannan

Assha: Na Kusa Da Buhari Sun Fi Damuwa Da Batun Sauyin Kudi, Minista Ya Bayyana Gaskiyar Abin da Ke Ransa

Shugaban 'yan bindiga ya ce ya mallaki sabbin kudi
Mun Siya Makamai da Sabbin Naira, Za Mu Yaki Gwamnati Dasu, Inji Shugaban ’Yan Bindiga Kachalla | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Manufar yin sabbin Naira

A baya, gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya bayyana cewa, daya daga cikin manufofin sauya fasalin N200, N500 da N1000 a Najeriya shine rage aikata ta’addanci a kasar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A fahimtar gwamnan, daina amfani da tsoffin kudaden zai sa ayyukan satar mutane da ta’addanci su ragu kasancewar samun kudin zai ba da wahala.

Sai dai, a wani bidiyon da aka yada, Balleri ya ce wannan sabuwar doka ta CBN talakawa kawai za ta wahala, wadanda aka bari da kuncin ciyar da ahalinsu, Sahara Reporters ta ruwaito.

A cewarsa:

“Kabilanci ba zai warware matsalolin Najeriya ba. Adalci ne kadai zai warware matsalolin. Talakawa basu san abin da sauya fasalin Naira ke nufi ba.
“Wasu daga cikinsu basu da N10,000. Rayuwa suke daga hannu zuwa baka. Amma wadanda suka mallaki miliyoyi; matsalarsu ce.

Kara karanta wannan

Rudani: 'Yan Najeriya sun fusata, sun fara zanga-zanga sabuwa karancin sabbin Naira

“Da yawa daga cikin talakawan basu ma taba gamo da sabbin kudin ba. Amma wadanda ake yiwa kallon ‘yan ta’adda suna dasu tuli.
“Mun siya makamai da sabbin kudaden don mu yake su. Yanzu muna jiran abin da za kuma su ce. Muna yin abin da muke yi ne saboda Allah da kuma talakawan da muke tare dasu, ba gwamnati ba. Bamu da matsala da duk wanda yake so ya mu’amalance mu da kyau.”

Mata ta mutu saboda karancin sabbin Naira

A wani labarin kuma, kunji yadda wata mata ta rasa ranta saboda babu sabbin kudi a garinsu gashi kuma ta fara nakuda.

Mijin matar ya bayyana cewa, ya nemi hanyar samun sabbin Naira a bankunan kasar nan, amma ya rasa saboda dalilai.

Har yanzu sabbin kudade basu fara yawa a hannun mutane ba, bankuna na ci gaba da kin ba da kudin ga ‘yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel