'Yan Sanda Sun Kama Mai Kai Wa ’Yan Bindiga Abinci da Bayanan Sirri a Jihar Neja

'Yan Sanda Sun Kama Mai Kai Wa ’Yan Bindiga Abinci da Bayanan Sirri a Jihar Neja

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta yi nasarar kame wani matashin da ke kai kayan abinci ga ‘yan bindiga a dajin jihar
  • An kama Ibrahim Ali ne dauke da kayayyakin abinci da ya nemo don kaiwa maboyar ‘yan bindigan da ke dajin Gwalo
  • Ya zuwa yanzu ana ci gaba da bincike don tabbatar da an gurfanar da matashin mai shekaru 24 a gaban kotu bayan gano gaskiya

Jihar Neja - Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta ce jami’anta da ke aiki a ofishin yanki na Gawu-Babangida sun yi nasarar kame wani matashi mai shekaru 24, Ibrahim Ali da aka fi sani da Bajala da ake zargin yana kai kayan abinci ga ‘yan bindiga.

Kama Bajala na zuwa ne bayan kama wasu mutum biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne a yankin Lambata a karamar hukumar Gurara a ranar 27 ga watan Janairun 2023, Channels Tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Manya basu tsira ba: 'Yan bindiga sun tare motar kwamishinar mata, sun yi awon gaba da ita

'Yan sanda sun kama masu kai abinci ga 'yan bindiga
'Yan Sanda Sun Kama Mai Kai Wa ’Yan Bindiga Abinci da Bayanan Sirri a Jihar Neja | Hoto: platinumpost.ng
Asali: UGC

A cewar sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP WA Abiodun ya fitar, an kama Ibrahim Ali, wanda dan asalin yankin Gwalo ne a karamar hukumar Paikoro a ranar 1 ga watan Fabrairu.

Ina taimakawa ‘yan bindiga sace mutane

Ya bayyana cewa, Ibrahim ya amsa laifin da ya aikata bayan titsiye shi, kuma yace yakan kai wa ‘yan bindiga bayanai kan mutanen da za su sace, Platinum Post ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

DSP Abiodun ya ce, wanda aka kaman ya kuma amsa cewa, yakan taimakawa ‘yan bindigan wajen samo kayan abinci irin shinkafa, wake, gero da ma barasa da sauran kayayyaki.

Kakakin ya kara da cewa, an kama Ibrahim da wasu kayayyakin da suka hada da wake da shinkafa, wanda yace zai kai ne maboyar ‘yan bindiga da dajin Gwalo.

DSP Abiodun ya ce, a yanzu haka ana ci gaba da bincikar Ibrahim a sashen manyan laifuka na SCID da ke Minna kafin gurfanar dashi a gaban kotu bayan gama bincike.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Daba Sun Yi Garkuwa da Ɗan Takarar Gwamnan APC a 2023

An kama masu kai wa 'yan bindiga makamai a Zamfara

A wani labarin kuma, a jihar Zamfara an kama wata mota makare da kayayyakin abinci da kwayoyi da ake shirin kai wa 'yan bindiga.

Hakazalika, an kama bindigogi da sauran manyan makanan aikata laifuka daga motar da aka kaman.

Mutum takwas hukuma tace ta kama da ke da hannu a wnanan aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel