Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga Bakwai a Jihar Kaduna, Inji Ofishin Gwamnati

Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga Bakwai a Jihar Kaduna, Inji Ofishin Gwamnati

  • Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar fatattakar ’yan ta’adda a wani yankin jihar Kaduna a Arewa maso Yamma
  • An ce akalla ‘yan bindiga bakwai ne suka hallaka yayin da wasu suka samu munanan raunuka a farmakin na soji
  • Gwamnan jihar Kaduna ya yabawa sojoji bisa wannan gagarumin aikin da yace sun yi mazantaka wajen yinsa

Jihar Kaduna - Rundunar sojin kasa da na ruwa a Najeriya sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga bakwai a wani aikin da suka yi a yankin Kasso da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, inda yace sojojin sun gamu da ‘yan bindigan ne a kusa Unguwan Rimi da Kasso kusa wani rafi.

A cewarsa, fada mai tsanani ne yar barke tsananin ‘yan ta’adda da sojojin na Najeriya, har ta kai ga hallaka wasu daga cikinsu, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin bayani: An kone bankuna har biyu a wata zanga-zanga a wata jiha, cewar 'yan sanda

An hallaka 'yan ta'adda a jihar Kaduna
Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga Bakwai a Jihar Kaduna, Inji Ofishin Gwamnati | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewarsa, an kashe ‘yan bindiga biyu tare da cewa akwai yiwuwar wasu sun mutu ba a gansu ba wasu kuma sun samu munanan raunuka.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An kwato kayayyaki da yawa a hannun ‘yan bindiga, ciki har da babura biyar, harsasai 153 da wayoyin hannu guda uku da dai sauran kayayyakin aikata ta’addanci.

Martanin gwamnan jihar Kaduna bayan samun labarin abin da ya faru

Da yake martani bayan samun labarin aikin da aka yi, Aruwan ya ce, El-Rufai ya yaba tare da yiwa sojojin addu’a, Vanguard ta ruwaito.

A cewarsa:

“Da yake karbar rahoton, gwamna Nasir El-Rufai ya yabawa jami’an tsaron bisa kokarinsu da jarumtarsu.
“Gwamnan ya yabawa shugabancin Manjo-Janar TA Lagbaja, GOC na yankin na daya da Cdre ME Ejumabone, kwamandan makarantar fasaha ta sojin ruwa bisa wannan nasarar aiki.”

Za a farmaki jirgin kasan Abuja-Kaduna, inji hukumar DSS

Kara karanta wannan

Matsayar Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi a kan batun Canjin N200, N500 da N1000

A wani labarin kuma, kun ji yadda hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta bayyana yadda ‘yan ta’addan Boko Haram ke shirin kai hari a Abuja ko Kaduna.

Hukumar ta ce, ana fargabar ‘yan ta’addan za su kai hari ne kan jirgin kasan Abuja-Kaduna da aka taba kaiwa hari shekarar da ta gabata.

Ya zuwa yanzu dai an yi kira ga masu ruwa da tsaki da su gaggauta daukar mataki kafin faruwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel