Kasashen Duniya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar farko zuwa kasar Faransa, wannan shi ne karon farko da shugaban zai fita waje tun bayan rantsar da shi a watan Mayu.
A ranar 24 ga watan Yuni za a zabi Shugaban kasa da 'Yan Majalisa a Sierra Leone. Tuni Yemi Osinbajo ya jagoranci tawagar kungiyar Commonwealth zuwa kasar.
A yammacin Talata, Dr. Goodluck Jonathan ya yi zaman farko da Bola Ahmed Tinubu bayan hawansa kan mulki. Tsohon Shugaban Najeriyan ne wakilin ECOWAS a Mali.
Akwai kasashe marasa girma a Afrika duk irin yalwar kasar da nahiyar da kasashenta kamar su Aljeriya, Kongo, Sudan. Fadin Seychelles bai wuce kilomita 1500 ba.
Fadar White House ta ce Shugaban kasar Amurka, Joseph R. Biden Jr. ya zabi tawagar da za ta zo Najeriya wajen rantsar da sabon shugaban kasa da za ayi a Abuja.
Wata kyakkyawar Bahaushiya ƴar Najeriya, ta shiga cikin jerin sojojin ƙasar Amurka. Budurwar ta zama cikakkiyar sojan Amurka ne bayan sun kammala samun horo.
A jiya, Antony Blinken ya dauki kimanin minti 20 yana zantawa da zababben shugaban Najeriya. Mataimakin Kakakin Jakadancin Amurka, Matthew Miller ya fadi haka.
Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana yadda aka yi nasarar kawo karshen annobar Korona da ta addabi duniya a shekarun da suka gabata kadan da suka dame wa kowa.
An harbi jirgin kasar Turkiyya da ya je kwashe ’yan kasar da suka makale a Sudan bayan bangarorin da ke yakar juna sun amince su kara tsagaita wuta na awa 72.
Kasashen Duniya
Samu kari