São Tomé & Príncipe da Jerin Kasashe 7 Mafi Karancin Girma cikin Afrika

São Tomé & Príncipe da Jerin Kasashe 7 Mafi Karancin Girma cikin Afrika

  • A duk Duniya, Afrika ce nahiya mafi yawan al’umma bayan Asiya, tana da girman kilomita miliyan 30
  • Tun a shekarar 2018 akwai mutum fiye da biliyan 1.3 da ke rayuwa a nahiyar da ke dauke da bakin fata
  • Duk fadin Afrika, akwai wasu kasashe masu karancin girma, a kan tudu Gambiya ce mafi kankantarsu

A wannan rubutu, mun kawo jerin kasashen Afrika masu karancin girman kasa. The Guardian ta fitar da irin wannan rahoto a shekarun baya.

Su wanene wadannan kasashe?

1. Seychelles

Seychelles, tsibiri ne a gabar Tekun Indiya da Ruwan Somaliya, girman tsibirin bai wuce kilomita 1500 ba. Mazauna kasar kimanin 100, 000 ne.

2. São Tomé and Príncipe

A Afrika kasa ta biyu a kankanta ita ce São Tomé and Príncipe. Kasar mai girman 964 km2 tana kan iyaka da Gabon tana da mutane 201, 800.

Kara karanta wannan

Muna zuba muku ido: Kungiyar Islama ta ce za ta barranta da 'yan siyasar da ba sa amfanar Musulmai

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

3. Mauritius

Kamar yadda jaridar ta kawo jerin kasashe marasa girma, Mauritius wani tsibiri mai kilomita 2000 a kudu maso gabashin nahiyar shi ne na uku.

4. Comoros

Wani kankanin tsibirin shi ne Comoros a kusa da kasashen Mozambique da Madagascar. Ana lissafi mazauna kasar ba su wuce 800, 000 ba.

Kasashe Mafi Karancin Girma
Kasashen Afrika marasa girma Hoto: the-travelling-twins.com
Asali: UGC

5. Cape Verde

Cape Verde kasa ce maras girma kuma maras yawan al’umma (akwai mutane kimanin rabin miliyan). Girman ta bai wuce kilomita square 4000 ba.

6. The Gambia

Kasar Gambiya a yammacin Afrika tana cikin marasa girma a fadin nahiyar da kilomita square 10, 380 kamar yadda Wikipedia suka tabbatar a shafinsu.

Sauran kasashen da ke wannan rukuni su ne:

7. Swaziland (Eswatini)

8. Djibouti

9. Ruwanda

10. Burundi

11. Equatorial Guinea

12. Lesotho

13. Guinea Bissau

14. Togo

15. Sierra Leonne

Najeriya za tayi sabon kudi

Kara karanta wannan

Ni ba barawo bane: Sanatan APC ya sharbi kuka a majalisa, ya fadi sharrin da aka masa

Kamar yadda Janar Muhammadu Buhari yayi a 1984, Gwamnan CBN, Godwin Emefiele yace za a fito da sababbin takardun kudi a shekarar bana.

An samu rahoton yadda tattalin arziki zai motsa a sanadiyyar wannan mataki ta fuskar karyewar Naira a kan Dala da tashin farashin kaya a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel