Kyakkyawar Bahaushiya Ta Zama Soja a Amurka, Bidiyonta Ya Yadu

Kyakkyawar Bahaushiya Ta Zama Soja a Amurka, Bidiyonta Ya Yadu

  • Wata kyakkyawar Bahaushiya ƴar Najeriya ta zama soja a ƙasar Amurka, bayan sun kammala horo mai tsanani
  • A cikin wasu bidiyoyi da ta sanya a TikTok da sunan @mrindiana1, budurwar ta yi magana cikin harshen Hausa na ɗan gajeran lokaci
  • Nan da nan bidiyon ya yaɗu, inda ƴan Najeriya da dama a TikTok suka garzaya wajen 'kwament' suna tayata murna

Wata kyakkyawar Bahaushiya ƴar Najeriya ta kammala samun horo, sannan har ta zama soja a ƙasar Amurka.

Hakan ya bayyana ne a cikin wasu gajerun bidiyoyi da @mrindiana1 ya sanya a manhajar TikTiok.

A cikin bidiyon na farko, an nuna budurwar tsaye a cikin wani fili, tana riƙe da jakarta, yayin da ta ke ta murmushi cike da farin ciki.

Kyakkyawar Bahaushiya ta zama soja a Amurka
Kyakkyawar Bahaushiyar ta samu horo sosai Hoto: @mrIndiana1
Asali: TikTok

Ta na yin magana da wani ne daban wanda shi ma ya ke tayata murnar wannan nasarar da ta samu.

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Budurwa Ta Dukufa Neman Na Kanta, Mutane Da Dama Sun Jinjina Mata, Bidiyon Ya Dauki Hankula

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Budurwar ta fito daga wajen da aka kammala basu horo, kuma tana sanye ne cikin kayan sojoji, waɗanda suka mayar da ita ta zama kalar ba wasa kuma kyawunta ya ƙara bayyana.

Wani ne dai ya ke yi mata tambayoyi cikin harshen Hausa, kafin daga bisani su rikiɗe su koma harshen Turanci.

A cikin bidiyon na biyu, ta bayyana cewa kammala samun horon da ta yi, ya sanya ta ji kamar an sauke mata wani ƙatoton nauyi, inda ta bayyana cewa horon aikin soja akwai matuƙar wahala.

Ƴan soshiyal midiya sun yi tsokaci sosai

Mutane da yawa sun cikata da saƙonnin murna a ɓangaren yin 'kwament' na bidiyon.

Ga kaɗan daga ciki:

@Auwal Abdallah ya rubuta:

"Ina taya ki murna ƴar'uwa, muna alfahari da ke Masha Allah."

@abdulrasheed muham74 ya rubuta:

Kara karanta wannan

A sharar titi: Yadda wata mata ke hada sama da N860k a sana'ar shara

"Dan Allah ta yaya zan iya shiga sojan Amurka ne?"

@ACTOR and BOSS ya rubuta:

"Masha Allah, na yi matuƙar jindaɗi da na yi arba da ke."

@ALI ALHAJI MAAJI ya rubuta:

"Najeriya abar alfaharinmu....babu abinda babu a Najeriya......muna alfahari da ke ƴanmata."

Bidiyon Wasu Sabbin Ma'aurata Ya Kayatar

A wani labarin na daban kuma, wasu ma'aurata sun zo da sabon salo a wajen bikin aurensu. Ma'auratan dai sun gudanar da bikin aurensu a sauƙaƙe.

Hotunan bikin auren na su dai sun ɗauki hankulan sosai a soshiyal midiya, inda mutane suka yi ta muhawara a kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel