Shugaba Tinubu Zai Kai Ziyarar Farko Kasar Faransa Tun Bayan Darewa Kujerar Shugabancin Kasar

Shugaba Tinubu Zai Kai Ziyarar Farko Kasar Faransa Tun Bayan Darewa Kujerar Shugabancin Kasar

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar farko zuwa kasar Faransa a ranar Alhamis 22 ga watan Yuni don wani babban taro
  • Dele Alake, mai ba wa shugaban shawara akan ayyuka na musamman da kuma sadarwa shi ya bayyana haka a yau Litinin 19 ga watan Yuni
  • Ya ce Shugaba Tinubu zai yi ziyarar ce ta kwana biyu da za ta fara daga ranar Alhamis 22 zuwa Asabar 24 ga watan Yuni

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyararsa ta farko zuwa Faransa tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.

Wannan ita ce ziyararsa ta farko zuwa kasar ketare a matsayin shugaban kasa, wanda ake saran zai kai kwana biyu a Faransa.

Tinubu zai tafi kasar Faransa ziyara a karon farko
Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Channels TV.
Asali: Twitter

Channels TV ta tattaro cewa Tinubu zai gana da manyan shugabannin kasashen duniya a Paris.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: A Karshe, Tinubu Ya Gana Da Dangote, Bill Gates A Abuja, Ya Bayyana Inda Zaifi Bai Wa Fifiko

Tinubu zai kai ziyarar farko kasar Faransa

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai yi ziyarar ce a Faransa a ranar Alhamis 22 ga watan Yuni, ziyarar ta kwana biyu ce daga ranar Alhamis 22 zuwa Asabar 24 ga watan Yuni.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai ba shi shawara a ayyuka na musamman da sadarwa, Dele Alake shi ya bayyana haka inda ya ce shugaban zai gana da manyan shugabannin duniya a Faransa.

Alake ya bayyana haka a yau Litinin 19 ga watan Yuni ya ce shugabannin za su rattaba hannu a kan kudirin taimakon kudade da za a bai wa kasashe masu rauni fifiko.

Taimakon kudaden a cewarsa an yi ne don kawo sauki ga kasashen da suka fi shiga yanayi a lokacin cutar Korona da dumamar yanayi da kuma sauyin yanayi.

Shugaban Faransa, Macron shi ne mai masaukin baki

Kara karanta wannan

Zance ya fito: Bayan Ganawar Tinubu Da Dangote Da Matawalle, Batutuwa Sun Fito Waje

Taron zai samu jagorancin shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron a Palais Brongniart da ke kasar, cewar Vanguard.

A cewar sanarwar:

"Tinubu zai samu rakiyar mambobin kwamitin shugaban kasa na tsare-tsare da sauran manyan mukarraban shugaban kasa, Tinubu zai dawo kasar a ranar Asabar 24 ga watan Yuni."

Har Yau Peter Obi Ya Fi Tinubu, Atiku Cancanta, In Ji Obasanjo

A wani labarin, tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya ce har yanzu Peter Obi ya fi cancanta.

Obasanjo ya ce shi bai ga wanda ya kai ba tsakanin Tinubu da Atiku a zaben da aka gudanar.

Obasanjo ya bayyana haka ne a wata ganawarsa da dan jarida, Chude Jideonwo kamar yadda Legit.ng ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel