An Samu Nasara: Hukumar Lafiya Ta Duniya Ta Ce Yanzu Kam an Kawo Karshen Annobar Korona

An Samu Nasara: Hukumar Lafiya Ta Duniya Ta Ce Yanzu Kam an Kawo Karshen Annobar Korona

  • Yanzu dai an tabbatar da ganin karshen annobar Korona da ta addabi duniya a shekaru uku da suka gabata
  • Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar da cewa, yanzu ba dole a mai da hankali kan annobar ba
  • Ya zuwa yanzu hukumar ta ce akwai barazanar ci gaba da samun matsalolin da ke alaka da annobar ta Korona

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce yanzu kam ya ayyana karewar annobar Korona da ta daidaita tattalin arzikin duniya.

Annobar Korona dai ta yi fice, inda ta tabbatar da karshen mutane da yawa a duniya a duniya tare da tsayar da harkoki daban-daban a kasashen duniya.

Bayan shekaru sama da 3 da barkewar cutar, WHO yanzu ta ce an ga karshen cutar da ta ayyana a matsayin annoba a baya.

Kara karanta wannan

Kungiyar Ibo Ta Najeriya Ta Ragargaji Gwamnatin Buhari Kan Hukuncin Ekweremadu, Ta Bayyana Mataki Na Gaba

Korona ta kare, inji WHO
Yadda annobar Korona ta girgiza duniya | Hoto: Daily Post Nigeria
Asali: Facebook

Wannan na fitowa ne daga baklin shugaban hukumar, Tedros Adhanom Ghebreyesus a jiya Juma’a, kana ya gargadi jama’a cewa, duk da haka ana ganin cutar a matsayin barazana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda aka cimma matsaya kan batun Korona

Kwamitin da WHO ta kafa na musamman domin kula da annobar Korona ne ya bayyana cewa, yanzu ba a bukatar mai da hankali kan annobar.

Kwamitin ya bayyana cewa, a halin yanzu an samu saukin yaduwar annobar da kuma tasirinta kan al’ummar duniya.

Duk da haka, shugaban WHO ya bayyana cewa, hadari da barazanar annobar Korona bai kau ba tukuna.

Adadin kisan da Korona ta yi a zamaninta

Ya kuma yi kiyasin cewa, annobar ya zuwa yanzu ya kashe mutane sama da miliyan 20 a duniya, kimamin rubi uku na adadin mutane miliyan 7 da aka ce ta hallaka a hukumance.

Kara karanta wannan

To fah: Tinubu ya tafi ganawa da gwamnan PDP, kwamitin NWC na APC ya shiga ganawa

A ranar 30 ga watan Janairun 2020, duniya ta shaida sanarwar WHO cewa, annobar Koron da ta samo asali daga China ta zama annoba a duniya makwanni kadan bayan barkewarta a Wuhan.

Dan takarar shugaban kasa a Najeriya ya kamu da Korona

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Dumebi Kachikwu, a ranar Jumu'a ya bayyana cewa ya kamu da cutar Korona da ta addabi duniya.

Mista Kachikwu ya yi kira ga 'yan Najeriya su yi takatsantsan domin akwai yuwuwar cutar ta sake dawowa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ba wannan ne karon farko da wasu jiga-jigan ‘yan siyasan Najeriya ke kamuwa da annobar Korona ba, an sha hakan a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel