Wani Mutum Ya Zauna A Otel Din Alfarma Tsawon Shekaru 2 Ya Tara Bashin N57m, Ya Tafi Bai Biya Ko Kwandala Ba

Wani Mutum Ya Zauna A Otel Din Alfarma Tsawon Shekaru 2 Ya Tara Bashin N57m, Ya Tafi Bai Biya Ko Kwandala Ba

  • Jami'an 'yan sanda sun bazama neman wani matashi da ya shafe shekaru biyu bai biya kudin hayar otal ba
  • Matashin mai suna Ankush Dutta ya tsere bayan kama hayar otal din tun shekarar 2021 amma ko sisi bai biya ba
  • Jimillar kudaden da ake bin Dutta sun kai N57m inda ya kwashe shekaru biyu ba a samun komai daga wurinsa

Delhi, Indiya - Wani matashi mai suna Ankush Dutta da ya zauna a otal na birnin Delhi ya shafe shekaru biyu ba tare da biyan ko sisi ba, hukumar otal din tana zarginshi da damfara.

Otal din ta bazama neman matashin tare da kai korafi akan ma'aikatansu kan barin matashin ba tare da ya biya kudin haya ba.

Matashi ya tsere a otal bayan shafe shekaru 2 bai biya sisi ba
Matashin Da Ya Tsere Bayan Shafe Shekaru 2 A Otal. Hoto: Getty Image.
Asali: Getty Images

Jaridar Indian Express ta tattaro cewa Dutta ya kama otal din Roseate a shekarar 2019 bayan ya tsawaita zaman nasa a watan Janairu na shekarar 2021.

Kara karanta wannan

Lauya Ya Kwana A Ofishin ’Yan Sanda Bayan Kama Shi Da Matar Aure A Otal, Ya Fadi Dalilin Haduwarsu

Ana bin matashin bashin N57m kudin otal din

Jimillar kudin da ake bin Dutta ya kai N57m bayan shafe shekaru biyu ba tare da biyan kudin hayar otal din ba, Legit.ng ta tattaro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hukumomin otal din na zargin Dutta ya hada baki da wani ma'akacinsu ne da ya taimaka masa ya boye yawan bashin da ake binsa ta hanyar gogewa.

A dokar otal din duk wanda ya suke bi bashin da yakai N300,000 dole ma'aikaci ya kai rahotonshi ga hukumomin otal din.

'Yan sanda sun bazama neman matashin da ya tsere

Korafin da aka kai wurin 'yan sanda ta ce:

"Bakon da kuma wasu ma'aikata sun kaucewa biyan kudin haya, ana binsu bashi yakai N57m yayin da suka goge rahoton zaman bakon a otal din.
"Ana zarginsu kuma da damfara wurin nuna takardu da shaidun bogi inda suka damfari otal din ta hanyar zamba.

Kara karanta wannan

Neja: Bene Ya Ruguje Tare Da Kashe Yaro Dan Shekara 15, Gwamnati Ta So Rushe Benen Kafin Yanzu

"Mun tabbatar daya daga cikin shugabannin ma'aikatan otal din mai suna Prem Prakash da sauya rahoto tare da goge duk shige da ficensa a kullum a ofishin da ake biyan kudin haya."

Yanzu haka 'yan sanda sun bazama neman Dutta wanda ake zargin ya damfari otal otal da dama a kasar India ba Roseate kadai ba.

Roseate otal ya kasance daga cikin otal masu tsada da ake biyan N80,000 a dare daya.

Lauya Ya Kwana A Ofishin ’Yan Sanda Bayan Kama Shi Da Matar Aure A Otal

A wani labarin, wani lauya ya bayyana yadda ya kwana a ofishin 'yan sanda bayan ganawa da matar aure a otal.

Lauyan mai suna Ayo Sogunro ya ce ya je Abuja ne saboda taron kare hakkin dan Adam lokacin da abin ya faru.

Ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a ranar Laraba 21 ga watan Yuni inda ya ce ya kira abokansa don su hadu a otal din.

Asali: Legit.ng

Online view pixel