Alkawarin da Amurka Tayi wa Najeriya da Sakataren Gwamnati Ya Kira Tinubu a Waya

Alkawarin da Amurka Tayi wa Najeriya da Sakataren Gwamnati Ya Kira Tinubu a Waya

  • Antony Blinken ya dauki kimanin mintuna 20 yana zantawa da zababben shugaban Najeriya
  • Sakataren gwamnatin Amurkan ya yi alkawari kasarsa za ta ba Gwamnatin Bola Tinubu hadin-kai
  • Tunde Rahman ya ce mai gidansa ya shaidawa Amurka abubuwan da zai maida hankali a kan su

Washington - Sakataren gwamnatin kasar Amurka, Antony Blinken ya tabbatar da cewa za su yi aiki da Asiwaju Bola Tinubu domin karfafa alaka.

A wani jawabi da zababben shugaban Najeriya ya fitar, Vanguard ta ce Asiwaju Bola Tinubu ya tabbatar da yin waya da Antony Blinken a ranar Talata.

Tunde Rahman ya ce Sakataren na gwamnatin Shugaba Joe Biden ya shafe tsawon mintuna 20 yana zantawa da mai gidansa ta wayar salula a jiya.

Buhari da Tinubu
Bola Tinubu tare da Shugaban Najeriya Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Blinken ya shaidawa shugaba mai jiran gado za su hada-kai da shi domin taimakawa kasashen.

Kara karanta wannan

Gaskiyar Bayanan Zaman Kwankwaso, Tinubu, da Sanusi a Faransa Sun Fara Bullowa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jawabin da Tunde Rahman ya fitar, ya nuna shi kuma Bola Tinubu ya yi alkawarin zai kama aiki gadan-gadan da zarar an rantsar da shi a karshen wata.

Haka zalika, Tinubu ya sha alwashi gwamnatinsa da za a rantsar a ranar 29 ga watan Mayun 2023 za tayi kokari wajen samun alaka mai kyau da Amurka.

Jawabin ofishin Bola Tinubu

“Asíwájú Tinubu ya yi magana da Sakataren gwamnatin Amurka, Antony Blinken ta wayar salular da wani Jakadan Amurka ya hada.
An yi zantawar ne cikin fadan gaskiya da kuma wasa da dariya a yammacin ranar Talatar nan.
Zababben shugaban kasar ya ce abin da zai fara da su su ne gyara hukumomin gwamnati da kawo tsare-tsaren da za su inganta siyasa da taimakon marasa karfi.
Sannan ya nuna shirinsa na karfafa damukaradiyyar Najeriya tare da bautawa mutane a matsayinsa na shugabansu.

Kara karanta wannan

Kwanaki 13 Kafin Ya Bar Aso Villa, Buhari Ya Fadi Kokari 3 da Ya Yi Cikin Shekaru 8

- Tunde Rahman

Karin bayani daga Jakada

Ofishin Jakadancin Amurka ta tabbatar da haka a wani jawabi da aka fitar. Blinken ya tabbatar da a sa ran alakar mutunta juna tsakaninsu da Najeriya.

Mataimakin Kakakin Jakadancin Amurka, Matthew Miller ya fitar da jawabin a shafin Twitter.

Kwankwaso da Tinub a Faransa

Rahoto ya zo cewa Bola Tinubu ya yi wa Rabiu Kwankwaso tayin kujerun Ministoci biyu a Gwamnatinsa, da alama zai kafa gwamnati da 'yan adawa.

Sanan Zababben shugaban kasar ya sa labule da tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II. Zuwa yanzu ba a iya gane manufar zaman da aka yi a Faransa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel