Bola Tinubu Ya Haɗu da Shugaban Kasar Benin, Ya Taɓo Batun Iyakoki da Kasuwanci

Bola Tinubu Ya Haɗu da Shugaban Kasar Benin, Ya Taɓo Batun Iyakoki da Kasuwanci

  • Bola Ahmed Tinubu ya nuna zai inganta alakar da ke tsakanin Najeriya da makwabciyarta Benin
  • Sabon shugaban kasar ya kyankyasa wannan ne a lokacin da ya zauna da Patrice Talon a kasar Faransa
  • Tinubu ya na ganin dole sai kasashen Afrika sun hada-kai sannan a samu bunkasar tattalin arziki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Paris - A ranar Juma’ar nan, Bola Ahmed Tinubu ya shaida cewa Najeriya ta shirya aiki da Jamhuriyyar Benin wajen samun cigaban kasuwanci.

Punch ta rahoto Shugaban kasar ya na cewa Najeriya da Benin su na bukatar juna musamman a bangarorin tsaro, kasuwanci da kula da iyakoki.

Bola Ahmed Tinubu da Patrice Talon
Bola Tinubu da Shugaban Kasar Benin, Patrice Talon Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter
"Dole mu fahimci cewa mu na bukatar junanmu. Mu na zagaye tare, ka da wani ya raba mu.
Na yi imani cewa a Afrika, ya zama dole mu kawowa nahiyar cigaba. Tattalin arzikin Duniya ya girgiza, kuma an bar Afrika a baya."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: A Karshe Tinubu Ya Magantu Kan Dakatar Da Emefiele, Ya Ba Da Hujja Mai Karfi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

- Bola Tinubu

Tinubu ya gana da Talon

Mai girma Bola Tinubu ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya yi zama da shugaban Benin, Patrice Talon, bayan taron da aka gudanar dazu a kasar Faransa.

Mai taimakawa shugaban Najeriyan wajen sadarwa, dabaru da harkoki na musamman, Dele Alake ne ya fitar da jawabin dazu daga birnin Faris.

Alake ya yi wa jawabin Mai gidan na sa da take da cewa “Manufofin tattalin arziki da huldatayyar kasar wajen Najeriya su na matukar bukatar Afrika.”

Danjuma ne 'Dan jummai

Tinubu ya ke cewa Najeriya da Benin tamkar tawage ne da su ke like da juna ta kugu, kuma su na samun taimako daga sauran kasashen da ake abokantaka.

Jawabin ya ce ce shugaban kasar ya fadawa takwaransa Talon cewa gwamnatinsa za ta bude hannunuwanta ga duk kasashen da ake makwabtaka da su.

Kara karanta wannan

Tinubu: Tsare-Tsaren Sabon Shugaban Najeriya Na Daukar Idon Duniya – Birtaniya

Mai girma Tinubu ya sanar da shugaban na Benin ya nada Adewale Bashir Adeniyi a matsayin shugaban hukumar kwastam domin hadin-kan kasashen.

Matsayar Shugaba Talon

Da yake na shi jawabin a Faris, Shugaba Talon ya ce ya ji dadin yadda Tinubu ya sha alwashin bada gudumuwa a kan harkokin tsaro da na kasuwanci.

A shirye Benin ta ke da tayi aiki da Najeriya musamman a sha’anin iyakoki, Talon ya ce Benin za ta haramta duk wasu abubuwan da Najeriya ta haramta.

An bude iyakar Seme

Rahoto ya zo cewa watakila daga yanzu motoci za su rika barkowa ta iyakokin Najeriya daga kasashen waje kamar yadda aka saba a shekarun baya.

Hana shigo da motoci ta kasa ya jawo Kwastam ta ga kudin shiga da ta ke samu ya ragu. Tsarin da Muhammadu Buhari ya fito da shi bai yi wa wasu dadi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel