Jihar Kano
Biyo bayan rikicin da ya mamaye Kano, Sheikh Dahiru Bauchi ya nuna rashin jin dadi kan matakin da gwamnatin Kano ta dauka na nada sabon sarki duk da umarnin kotu.
Masarautar Bichi ta yabawa Shugaba Bola Tinubu da kuma kokarin jami'an tsaro da bangaren shari'a wurin tabbatar da zaman lafiya a Kano yayin da ake cikin wani hali.
Wata kungiyar Arewa, 'Arewa Social Contract Initiative' ta roki Sarki Aminu Bayero (da aka tube) da ya bar jihar Kano yanzu domin a samu zaman lafiya a jihar.
Jami'an tsaro sun dauki matakin kulle hanyar da ke zuwa fadar da Alhaji Aminu Ado Bayero yake zaune a Kano. Hakan na zuwa ne yayin da ake takaddama kan sarautar Kano
Rahotannin da muke samu yanzu daga jihar Kano na nuni da cewa zanga-zanga ta barke a karamar hukumar Gaya domin nuna adawa ga gwamnati kan rusa masarautu.
Kungiyar matasan Arewa ta aika da wasika ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan rikicin sarautar da ke faruwa a jihar Kano. Ta bukaci ya yi taka tsan-tsan.
Kungiyar 'yan kasuwan Kano sun shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya mutunta umarnin babbar kotun tarayya wanda ya hana shi nada sabon Sarkin Kano.
Gwamnatin jihar Kano ta musanta jita-jitar da ake yadawa cewa ta samu takardar umarnin kotu kan tube sarakuna biyar da Gwamna Abba Kabir ya yi a jihar.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya soki matakin gwamnatin tarayya na tura sojoji kan rikicin masarautar Kano tsakanin Sanusi II da Aminu Ado.
Jihar Kano
Samu kari