Sarkin Kano: 'Yan Kasuwa Sun Ba Gwamna Abba Shawara Kan Abin da Ya Kamata Ya Yi

Sarkin Kano: 'Yan Kasuwa Sun Ba Gwamna Abba Shawara Kan Abin da Ya Kamata Ya Yi

  • Ƙungiyar ƴan kasuwan Kano ta aike da sako ga Gwamna Abba Kabir Yusuf kan tsige sarakuna guda biyar da ya yi a jihar
  • Ƙungiyar ta buƙaci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma bi umarnin babbar kotun tarayya wanda ya hana soke dokar masarautun Kano ta shekarar 2019
  • Shugaban ƙungiyar Usman Auwal Nagode ya ce yana da kyau Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zama mai mutunta doka

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - An buƙaci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya bi umarnin babbar kotun tarayya da ta hana gwamnatinsa soke dokar masarautun Kano ta 2019.

Ƙungiyar ƴan kasuwan Kano ta bayar da wannan shawarar ne a cikin wata sanarwa da shugabanta Usman Auwal Nagode ya fitar.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Atiku ya yi magana kan rikicin sarautar Kano, ya fadi mai laifi

'Yan kasuwa sun ba Gwamna Abba shawara
'Yan kasuwa sun bukaci Gwamna Abba ya bi umarnin kotu kan rikicin sarautar Kano Hoto: Sanusi Lamido Sanusi/Abba Kabir Yusuf/@Super_Joyce1
Asali: UGC

Ƙungiyar na magana ne dai dangane da rikicin sarauta tsakanin sabon Sarkin Kano, Muhamadu Sanusi II da tuɓaɓɓen Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Wace shawara aka ba Gwamna Abba?

Usman Nagode ya jaddada muhimmancin da ke akwai na Gwamna Abba ya mutunta doka, inji rahoton jaridar Vanguard.

Ya buƙaci dukkanin ɓangarorin gwamnati da su haɗa kai cikin lumana domin tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba a jihar Kano.

A cewar rahoton jaridar The Nation, shugaban ƙungiyar ya yabawa ɓangaren shari'a da hukumomin tsaro bisa bin doka da oda da tabbatar da cewa zaman lafiya ya dawo jihar.

“A madadin ƙungiyar ƴan kasuwan Kano, muna kira ga gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusif da ta mutunta tare da bin umarnin babbar kotun tarayya."

Kara karanta wannan

Abubuwa sun caɓe, jami'an tsaro sun mamaye gidan gwamnatin jihar Kano

"Wannan yana da matukar muhimmanci domin gujewa ƙara jefa al’ummar Jihar Kano cikin wahala, waɗanda tuni suka sha wahala sosai."
"Muna yabawa ɓangaren shari’a da hukumomin tsaro bisa bin doka da oda da kuma tabbatar da cewa zaman lafiya ya dawo jihar."

- Usman Auwal Nagode

Maganar Atiku kan rikicin sarautar Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi magana kan rikicin da ke faruwa dangane da sarautar Kano.

Atiku ya cacccaki matakin gwamnatin tarayya na tura sojoji zuwa cikin birnin yayin da ya yi nuni da cewa Gwamna Abba bai saɓa doka wajen naɗa Muhammadu Sanusi II.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng