Rikicin Masarautar Kano: Sheikh Dahiru Bauchi Ya Aika Muhimmin Sako Ga Abba

Rikicin Masarautar Kano: Sheikh Dahiru Bauchi Ya Aika Muhimmin Sako Ga Abba

  • Sheikh Dahiru Bauchi ya nuna rashin jin dadinsa kan matakin da gwamnatin Kano ta dauka na nada sabon sarki duk da umarnin kotu
  • Sheikh Dahiru ya nemi masu ruwa da tsaki a rikicin masarautar Kano da su mutunta umarnin babbar kotun tarayya domin zaman lafiya
  • Ya kuma tunatar da gwamnan Kano, Abba Yusuf cewa shi ma ya tabbata a kan kujerar gwamna ne saboda hukuncin kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Bauchi - Shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a rikicin masarautar Kano da su mutunta umarnin babbar kotun tarayya.

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi magana kan rikicin masarautar Kano
Sheikh Dahiru Bauchi ya nemi gwamnatin Kano ta bi umarnin kotu kan nada sabon sarki. Hoto: ShekhDahiruBauchi, EngrAbbaKYusif, sanusilamidoofficial
Asali: Facebook

Mun ruwaito babbar kotun tarayyar ta umarci gwamnatin jihar Kano da ta dakata daga aiwatar da sabuwar dokar da ta rusa masarautar Kano ta 2019.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano: Zanga zanga ta barke a fadar masarautar Gaya da majalisa ta rusa

Sheikh Dahiru ya aika sako ga Abba

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wannan kiran ne ne a bayan gwamnatin Abba Yusuf ta tsige sarakunan Kano tare da dawo da Sarki Muhammad Sanusi II, in ji rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi magana ne ta bakin shugaban gidauniyar Dahiru Bauchi, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi a wani taron manema labarai a Bauchi ranar Lahadi.

Jaridar Independent ta ruwaito shehin malamin ya tunatar da Gwamna Abba cewa shi ma ya samu mulkin jihar ne bayan kotu ta yi masa adalci a karshe.

"A mutunta umarnin kotu" - Sheikh Dahiru

A cewar Sheikh Dahiru Bauchi:

"Babu wanda ya fi karfin doka komai girmansa, don haka akwai bukatar gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da zaman lafiya da adalci a jihar tare da kaucewa abin da zai haifar da rikici.

Kara karanta wannan

Sarki 2 a lokaci 1: Lauyoyin Kano sun fitar da jawabi ganin an jibge jami'an Sojoji

“Tunda kotu ta shiga tsakani, to akwai bukatar kowane bangare ya mutunta doka domin zaman lafiya.
"Ba daidai ba ne gwamnatin jihar Kano ta yi gaban kanta ta nada sabon Sarkin Kano, tare da tube sarakunan jihar biyar duk da umarnin kotu”.

An nada sabon sarki duk da umarnin kotu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya nada sabon sarki duk da babbar kotun tarayya ta dakatar da shi daga yin hakan.

Abba ya tabbatar da nadin Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano bayan rusa masarautu biyar na jihar da kuma dawo da tsarin sarki daya a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.