"Ba Mu Cancanci Haka Ba": Masarautar Bichi Ta Magantu Yayin da Ta Yabi Jami'an Tsaro

"Ba Mu Cancanci Haka Ba": Masarautar Bichi Ta Magantu Yayin da Ta Yabi Jami'an Tsaro

  • Masarautar Bichi ta yabawa kokarin jami'an tsaro da bangaren shari'a wurin tabbatar da zaman lafiya a Kano
  • Masu ruwa da tsaki a masarautar sun kuma yabawa Shugaba Bola Tinubu kan nuna adalci da bin doka
  • Masarautar ta ce babu wani laifi da ta yi ga majalisar jihar ko gwamnatin Kano da suka cancanci wannan hukunci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Masarautar Bichi a jihar Kano ta magantu kan matakin da Gwamnatin jihar ta ɗauka kan masarautun.

Masu ruwa da tsaki a masarautar sun yabawa jami'an tsaro da kuma bangaren shari'a kan dogewa wurin tabbatar da kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano: Zanga zanga ta barke a fadar masarautar Gaya da majalisa ta rusa

Masarautar Bichi ta yi martani kan rikicin sarautar Kano
Masarautar Bichi ta koka kan yadda aka yanke danyen hukunci a Kano. Hoto: Aminu Ado Bayero, Abba Kabir Yusuf, Masarautar Bichi.
Asali: Facebook

Sanarwar da masarautar Bichi ta fitar

Nasiru Ado Bayero shi ke jagorantar masarautar kafin rusa su a ranar Alhamis 23 ga watan Mayu, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da wasu daga cikin dattawan masarautar 39 suka sanyawa hannu.

"Masarautar Bichi tana godiya matuka ga bangaren shari'a da kuma jami'an tsaro kan yadda suka tsaya wurin tabbatar da bin doka a wannan lamari."
"An tauyewa mutanen Bichi da masarautarta hakkinsu amma kokarin jami'an tsaro da bangaren shari'a ya dakile tashin hankali a masarautar da ma sauran masarautun guda hudu."
"Babu tantama dukkan masarautun guda hudu sun samu ci gaba a shekaru takwas da suka wuce ba tare da aikata wani laifi da suka cancanci wannan hukunci daga majalisa da kuma gwamnatin jihar ba."

- Masarautar Bichi

Har ila yau, masu ruwa da tsakin sun godewa Shugaba Bola Tinubu kan nuna adalci da bin doka a lamarin, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci sun magantu kan rawar jami'an tsaro da shari'a a rikicin sarautar Kano

Masu ruwa da tsakin masarautar Bichi

1. Mal Bello Salisu

2. Alh Uba Kunchi

3. Alh Sule Mu’azu Kunchi

4. Mal Muhammad Garba Yusuf

5. Alh Mudassir Ado Kunchi

6. Alh Tukur Sani Kwa

7. Mal Kabiru Muhammad

8. Alh Musa Zangon Mata

9. Sani Alasan Dawaki

10. Alh Ado Rabiu Danbayero

11. Alh Mohd Abba Danbatta

12. Alh Yahaya Nuhu

13. Alh Magaji Sani Maidaji

14. Alh Ibrahim Nuhu Amasaye

15. Alh Muntari Sale

16. Alh Danasabe Makoɗa

17. Alh Rabiu Abubakar Makoɗa

18. Mal Yusuf Yusuf Lawan

19. Alh Suleiman Ahmed Auwal

20. Hon Ibrahim Damisawa

21. Alh Babangida Mansur Kunya

22. Alh Murtala Rufa’i

23. Mal Musa Mai Azara

24. Alh Muhd Sani Gadanya

25. 18.Alh Ibrahim Zakari Bagwai

26. Alh Muhammad Inuwa Dabgaɗa

27. Alh Lawan Safiyanu Gogori

28. Alh Sunusi Nassarawa

29. Alh Jibirin Harbau

30. Alh Hamza Tsanyawa

31. Alh Nura ‘Yanchibi

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci sun tsoma baki a rikicin sarautar Kano, sun gargadi Tinubu

32. Alh Farouk ‘Yanganau

33. Alh Inusa Yusha’u Tsanyawa

34. Gwani Abdullahi Dangwani

35. Comrd Aminu Abdurrahman

36. Eng Bello Gambo Bichi

37. Barr Imam Ghazali Umar

38. Alh Aminu Abdulhamid

39. Alh Bello Gambo Gogori

Ribadu ya fusata kan zarginsa a Kano

Kun ji cewa, Mallam Nuhu Ribadu ya yi barazanar maka mataimakin gwamnan jihar Kano a kotu kan kalamansa.

Ribadu ya dauki matakin ne kan zarginsa da aka yi da hannu a ruruta rikicin jihar Kano wanda Abdulsalam Aminu Gwarzo ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.