Rikicin Masarauta: 'Yan Sanda Sun Bankado Shirin Tada Tarzoma a Kano, Sun Yi Gargadi

Rikicin Masarauta: 'Yan Sanda Sun Bankado Shirin Tada Tarzoma a Kano, Sun Yi Gargadi

  • Ƴan sanda a jihar Kano sun ce sun gano wani shiri da ɓata gari ke yi na tayar da tarzoma a jihar kan rikicin masarautar Kano
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar wanda ya bayyana hakan ya ce ɓata garin na shirin kai hare-hare a wasu muhimman wurare a cikin ƙwaryar birnin Kano
  • Ya yi gargaɗin cewa ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen cafke duk wanda aka samu da hannu a yunƙurin kawo hargitsi a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - A yayin da ake ta cece-kuce a kan rikicin masarautar Kano, hukumomin tsaro a jihar Kano sun ce sun gano wata maƙarƙashiyar tayar da tarzoma a jihar.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano - Jami'an tsaro sun dauki mataki kan Aminu Ado Bayero

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Usaini Gumel wanda a tare da shi akwai shugabannin hukumomin tsaro na DSS, NSCDC da sauransu ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai.

'Yan sanda sun gano shirin kawo rikici a Kano
'Yan sanda sun bankado yunkurin tayar da tarzoma a Kano Hoto: Kano State Police Command
Asali: Facebook

CP Usaini Gumel ya ce sun gano shirin kai hari kan majalisar dokokin jihar Kano da wasu fitattun wurare a jihar, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin tayar da tarzoma a Kano

Kwamishinan ƴan sandan ya ci gaba da cewa, za a gudanar da bincike gida-gida domin kamo ɓata garin da ke shirin haifar da tarzoma da kuma kawo tabarbarewar zaman lafiya a jihar, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"Mun samu sahihan bayanan sirri kan wasu gungun mutane waɗanda maƙiyan jihar nan ne tare da wasu ɓata gari masu ƙoƙarin tayar da hargitsi a jihar ta hanyar kai hare-hare a wasu wurare."

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Atiku ya yi magana kan rikicin sarautar Kano, ya fadi mai laifi

"Suna son kai hare-haren ne musamman a majalisar dokokin jiha da wasu muhimman wurare a cikin ƙwaryar birnin Kano. Majiyoyi da yawa sun tabbatar da wannan bayanan."
"Mun shirya tsaf domin fara aikin sintiri tare da gano wuraren da musamman aka gaya mana ɓata garin suke ɓoyewa."

- CP Usaini Gumel

Wane gargaɗi ƴan sanda suka yi

Kwamishinan ƴan sandan ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu da hannu a yunƙurin tayar da zaune tsaye za a kama shi domin ya fuskanci fushin doka.

Ya kuma bayyana cewa za su riƙa bi gida-gida domin nemo waɗanda suke tunanin sun fi ƙarfin doka.

Zanga-zanga ta ɓarke a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa zanga-zanga ta ɓarke a wasu sassa na Kano a ranar Lahadin nan kan matakin da gwamnatin jihar ta dauka na maido da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

A Gaya da Nasarawa inda aka gudanar da zanga-zangar, al’ummar garuruwan sun mamaye tituna domin nuna adawa da dawo da Sanusi II kan karagar mulki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel