Jihar Kano
Farfesa Ibrahim Muazzam, tsohon shugaban Hisbah ya bayyana yadda 'yan siyasa suka yi kokarin kawo rudani tsakanin hukumar da gwamnatin jihar kan ayyukan hukumar.
Sheikh Sa’id Aliyu Maikwano ya dauki wata matsaya da ta bambanta da ta sauran malamai, soki Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa yayin da rikicin Hisbah ta lafa a Kano.
A jihar Kano, jami’an NSCDC sun damke ‘dan shekara 85 da zargin garkuwa da mutane. Idan dai gaskiya ne, da alamu tsufa tayi wa wannan mutumi gardama.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya rantsar da alkalai 9 na babbar kotun jihar Kano da kuma khadi 4 na kotun ɗaukaka ƙara ta shari'ar musulunci.
Hukumar Hisbah ta kasance tana kira wajen gyara tarbiyya da yin kira zuwa ga koyarwar addinin musulunci a tsakanin al'ummar musulmai. Tana ayyuka da dama.
Babbar kotu da ke jihar Kano ta dauki mataki kan gwamnatin jihar da majalisa inda ta dakatar da su kan gyaran fuska a dokokin wasu hukumomi guda uku.
Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin ɗan shugaban jam'iyyar APC, Dakta Umar Ganduje, Umar Abdullahi Umar a matsayin babban darektan ayyuka a hukumar REA.
Hukumar tsaron farar hula (NSCDC) ta kama wani dattijo mai shekaru 85 mai suna Ibrahim Usman da ake zargi da yin garkuwa da wani yaro dan shekara 3 a Kano.
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirinta na cimma matakin tara kuɗaɗen shiga da suka kai Naira biliyan 10 duk wata a jihar, shugaban KIRS ya yi jawabi kan haka.
Jihar Kano
Samu kari