Rikicin Masarautar Kano: Rundunar Sojoji Ta Fadi Dalilin Tura Jami'anta

Rikicin Masarautar Kano: Rundunar Sojoji Ta Fadi Dalilin Tura Jami'anta

  • Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana rawar da jami'anta suka taka a rikicin da ake yi kan masarautar Kano
  • Kakakin rundunar ya bayyana cewa jami'an sojoji ba su da hannu a rikicin kuma ba su je fada ba domin tabbatar da umarnin kotu
  • Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya yi nuni da cewa an tura jami'an sojojin ne domin hana ɓarkewar rikici da tayar da hankula a jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Rundunar sojojin Najeriya ta musanta cewa akwai hannunta a rikicin masarautar Kano.

Kakakin rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya bayyana cewa sojojin ba sun je ba ne domin tabbatar da umarnin kotu kan rikicin masarautar Kano.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano - Jami'an tsaro sun dauki mataki kan Aminu Ado Bayero

Sojoji sun musanta hannu a rikicin masarautar Kano
Rundunar sojoji ta ce ba hannunta a rikicin masarautar Kano Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta ce kakakin rundunar sojojin ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce saɓanin abin da ƙungiyar lauyoyi ta jihar Kano ta faɗi, jami'an sojojin ba su da hannu a rikicin masarautar Kano kuma ba su da hannu a wajen tabbatar da umarnin da kotu ta ba da.

Kano: Meyasa aka tura sojoji?

Ya yi nuna da cewa matakan da rundunar ta ɗauka, ta ɗauke su ne domin hana karya doka da oda, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

"Sojoji sun ɗauki matakai ne kawai domin hana yiwuwar karya doka da oda da ka iya faruwa saboda rikicin masarautar Kano."
"Abu mai matuƙar muhimmanci ga rundunar sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro shi ne hana karya doka da oda a jihar, wanda wasu ɓata gari ka iya amfani da wannan damar."

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Atiku ya yi magana kan rikicin sarautar Kano, ya fadi mai laifi

- Manjo Janar Onyema Nwachukwu

Ya yi nuni da cewa sojoji za su shiga cikin lamarin lokacin da ƴan sanda suka kasa shawo kan yanayin da ake ciki kan tsaro a jihar.

Shirin tayar da tarzoma a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bankaɗo wani shirin tayar da tarzoma da wasu ɓata gari ke shirin yi a jihar.

Rundunar ta yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu da hannu a cikin wannan mummunan shirin za a cafke shi domin ya fuskanci fushin hukuma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel