Kwana 2 da Karbar Mulki, Sarki Sanusi II Ya Nada Sabuwar ‘Jakadiyar Sarkin Kano’

Kwana 2 da Karbar Mulki, Sarki Sanusi II Ya Nada Sabuwar ‘Jakadiyar Sarkin Kano’

  • Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya nada Hajiya A’in Jafaru Fagge a matsayin Jakadiyar Sarkin Kano
  • Wannan nadin na zuwa ne kwanaki biyu bayan da Muhammadu Sanusi II ya koma kan karagar sarautar Kano
  • A hannu daya, zanga-zanga ta barke a wasu sassa na jihar Kano inda ake kira ga gwamnati da ta tsige Sarki Sanusi II

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Kwanaki biyu da hawa kan kujerar mulki, sabon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya fara yin sauye-sauye ga hadiman cikin fada.

An nada Jakadiyar Sarkin Kano
Sarki Sanusi II ya nada Hajiya A'in Jafaru mukamin ‘Jakadiyar Sarkin Kano’. Hoto: @babarh
Asali: Twitter

An nada Jakadiyar Sarkin Kano

A yau Lahadi, muka samu rahoton cewa mai martaba Sanusi II, ya nada Hajiya A’in Jafaru Fagge a matsayin Jakadiyar Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

"Ka hakura da zaman Kano": Kungiyar Arewa ta ba Sarki Aminu shawara bayan an tsige shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai tallafawa gwamnan jihar Kano ta fuskar kafofin sada zumunta, Abdullahi I. Ibrahim ya tabbatar da hakan a shafinsa na X.

Abdullahi I. Ibrahim ya wallafa cewa:

"Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya nada Hajiya A’in Jafaru Fagge a matsayin Jakadiyar Sarkin Kano."

Kalli sanarwar a nan kasa:

Jakadiyar Sarkin Kano: Mutane sun magantu

Mutane sun yi martani kan wannan nadi na jakadiya.

@Usman_Tokari:

"Babu 'capacity' yar siyasa a fada"

@shamsumailowco1:

"Hajiya muna taya murna"

@nazeef___:

"Ba lokaci, Allah kawo namu nadin"

@isah_muaaz:

"Yan kwankwasiyya kuna sharafi wallahi, gwamnati ta ku, masarauta ta ku."

@ibrahimchicago:

"Agaishe ki jakadiya"

Zanga-zanga ta barke a sassan Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa zanga-zangar nuna adawa da mayar da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II kan kujerar mulki ta mamaye sassan jihar Kano.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya bayyana rawar da Tinubu ya taka wajen dawo da shi kan sarautar Kano

A Gaya da Nasarawa inda aka gudanar da zanga-zangar, al’ummar garin sun yi tururuwa a kan tituna domin nuna adawa da dawo da Sanusi II gidan sarautar Kano.

Masu zanga-zangar dai sun zargi gwamnatin jihar da yin amfani da wata manufa ta siyasa wajen rusa sarakunan biyar tare da neman a maido da masarautun nasu da kuma sarkin da aka tsige.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel