Wahalar man fetur a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu ya amince ana wahala a Najeriya, amma ya ce daina biyan tallafin fetur shi ne kawai matakin da zai kare Najeriya daga fadawa cikin fatara.
Wata mai yin sharhi, Titilope Anifowoshe ta yi hasashen cewa nan da watan Yunin 2024, farashin man fetur zai ragu zuwa tsakanin N570-N580 kan kowace lita.
Kamfanin mai na MRS Oil Plc ya sanar da rage farashin man dizal a dukkanin gidajen mai mallakinsa a fadin Najeriya biyo bayan rage farashi da matatar Dangote ta yi.
‘Yan kasuwa sun bayyana lokacin da ake tunanin daina ganin layi. Legit ta fahimci akwai layin fetur a irinsu gidajen man AYM Shafa da ke garin Zariya.
Rahotanni sun nuna cewa motoci aƙalla 100 ne ake tsammanin sun ƙone yayin da wasu tankokin man fetur suka fashe kuma suka kama da wuta a jihar Ribas.
Kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa Najeriya tana asara mai tarin yawa sakamakon gangar danyen man fetur 300,000 da ake sacewa a kullum.
Rahotanni sun nuna cewa ana cikin matsin ƙarancin mai yayin da ƴan bunburutu ke cin kasuwa yadda suke so, galan mai cin lita 5 ya kai N6000 zuwa sama.
Gwamnatin Jigawa ta fara daukan mataki a kan gidajen mai da suka kulle wurin kafa kwamitin kota kwana. Kwamitin zai rika zagawa domin tabbatar da mai ya wadata.
Mutane sun wayi gari cikin mawuyacin hali na ƙarancin man fetur a jihar Kaduna wanda ya sa ƴan bunburutu suka buɗe sabuwar kasuwa da farashi mai tsada.
Wahalar man fetur a Najeriya
Samu kari