Gwamnati Na Shirin Karya Farashin Iskar Gas Yayin Da ’Yan Najeriya Ke Korafin Farashin Ya Kai N1,300

Gwamnati Na Shirin Karya Farashin Iskar Gas Yayin Da ’Yan Najeriya Ke Korafin Farashin Ya Kai N1,300

  • Gwamnatin tarayya ta ce tana aiki tare da wasu masu ruwa da tsaki don tsara dabarun rage farashin gas din girki a kasar
  • Karamin ministan albarkatun man fetur ya ce matakin zai taimaka wajen iskar gas din ta wadata ga jama'a
  • Ya ce har yanzu Najeriya ba ta kai ga cim ma burinta na wannan gas din mai tsada ba, duk da kasancewarta kasa mai arzikin man fetur

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Gwamnatin tarayya ta yi taro da fitattun masu ruwa da tsaki a bangaren man fetur domin tsara dabarun rage farashin iskar gas din girki a fadin kasar nan.

Hakan ya faru ne yayin da farashin iskar gas din girki ya karu sosai daga kasa da naira 500 kan ko wane kilogiram a shekarar 2018 zuwa naira 1,300, lamarin da ya sa ‘yan kasar ke kuka.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da gobara ta kashe yaro dan shekara 4 a Jihar Kano

Karamin ministan man fetur ya ce gwamnati na shirin karya farashin gas din girki.
Karamin ministan man fetur ya ce gwamnati na shirin karya farashin gas din girki. Hoto: Kypros, Wilpunt
Asali: Getty Images

A yayin taron tuntubar masu ruwa da tsaki a Abuja, Ekperikpe Ekpo, karamin ministan albarkatun man fetur (Gas), ya bayyana aniyarsa ta rage farashin LPG.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iskar gas din girki za ta wadata

Ekpo ya ce, haɗin gwiwar zai taimaka wajen ba da tabbacin cewa gas din ya zama mafi sauƙin farashi, ya wadata, da kuma saukin samuwa ga jama'a, Businessday ta ruwaito.

Ya kara da cewa shigar masu ruwa da tsaki a harkar iskar gas na da nufin tabbatar da cewa harkar iskar gas ta kasa ta samu ci gaba mai dorewa.

Ya ce:

“Harkar makamashi yana samun ci gaba cikin sauri, kuma tattaunawarmu a yau za ta yi tasiri sosai ga al'ummomi masu zuwa. Dole ne mu kasance masu dabara da kawo sabbin abubuwa.

Abubuwan da ake jawo rashin fadada amfani da iskar gas

Kara karanta wannan

Talaka zai ji a jikinsa sakamakon tashin kudin shigo da kaya da aka yi wa Kwastam

Duk da cewa Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke da arzikin iskar gas, ya yi nuni da cewa har yanzu al'ummar kasar ba su fahimci karfin iskar mai tsadar gaske ba.

A cewarsa, akwai dalilai da yawa na rashin fadada amfani da iskar gas din girkin da suka hada da, rashin kyawun ababen more rayuwa, rashin daidaiton farashi, gibi a manufofi da tsare-tsare.

Sauran sun haɗa da rashin isassun kuɗi, matsalolin muhalli, yawaitar canjin makamashi mara kyau, da rashin cikakken tsarin haɓaka iskar gas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel