Bayan CBN da FAAN: Gwamnati Na Shirin Dauke Hukumar NUPRC Daga Abuja Zuwa Legas

Bayan CBN da FAAN: Gwamnati Na Shirin Dauke Hukumar NUPRC Daga Abuja Zuwa Legas

  • Shugaban hukumar da ke sa ido kan man fetur da iskar gas a Najeriya (NUPRC) ya kammala shirin mayar da wasu ofisoshin hukumar zuwa Legas
  • Wata majiya mai karfi ta ruwaito Mr Gbenga Komolafe na ikirarin cewa ya yi hakan don samar da sarari ga sabbin ma’aikatan da yake son ɗauka
  • Mayar da da wasu ofisoshin hukumar NUPRC zuwa Legas ya biyo bayan sauya shekar CBN da hukumar FAAN daga Abuja zuwa Legas

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar da ke sa ido kan man fetur da iskar gas a Najeriya (NUPRC) ta kammala shirin mayar da wasu sassan ta zuwa Legas daga Abuja.

Hakan ya biyo bayan sauya shekar da babban bankin Najeriya (CBN) ya yi a baya-bayan nan, tare da mayar da hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) zuwa Legas.

Kara karanta wannan

Mutane sun shiga fargaba sakamakon tashin abun fashewa a Legas, bidiyo ya bayyana

Bayan CBN da FAAN: Ana shirin mayar da hukumar NUPRC zuwa Legas.
Bayan CBN da FAAN: Ana shirin mayar da hukumar NUPRC zuwa Legas. Hoto: @NUPRCofficial
Asali: Twitter

Matakin na NUPRC zai sa sama da ma’aikata 200 na hukumar za su tashi daga Abuja zuwa Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayyukan da hukumar NUPRC ke yi a Najeriya

Ko a baya, matakin da gwamnati ta dauka na mayar da wasu sassan CBN da hedikwatar FAAN daga Abuja zuwa Legas ya janyo cece-kuce da rashin gamsuwa a tsakanin masu ruwa da tsaki.

Hukumar NUPRC, wacce a da ita ce Hukumar kula da albarkatun man fetur (DPR), wani bangare ne da ke karkashin ma’aikatar albarkatun man fetur ta tarayya (FMPR).

Tana sa ido kan masana'antar mai da iskar gas don tabbatar da bin ka'idoji da dokokin da suka dace, da kuma kula da fitarwa da shigo da kayayyakin cikin kasar.

Dalilin dauke hukumar daga Abuja zuwa Legas

Wata majiya mai karfi da ta zanta da Daily Trust ta ce:

Kara karanta wannan

EFCC: An daure Mama Boko Haram a kurkuku na shekaru 10 saboda zambar N40m

“Shugaban hukumar (CCE), Gbenga Komolafe ya fara yunkurin mayar da wasu sassan hukumar zuwa Legas.
“Ya yi iƙirarin cewa ya yi hakan don samar da sarari ga sabbin ma’aikatan da yake son ɗauka. Wannan kwata-kwata bai dace ba domin an mayar da ofishin zuwa Abuja daga Legas kasa da shekaru biyu da suka wuce."

Sabon hedikwatar da ke babban birnin tarayya, Abuja, mai hawa 10 ne wanda majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da shi a shekarar 2020.

Kokarin jin ta bakin kakakin hukumar, Misis Sonola don tabbatar da dalilin canja shekar ya ci tura domin ba ta dauki kira ko amsa sakon kar-ta-kwana ba.

Dalilin mayar da hukumar FAAN zuwa Legas

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa ministan sufurin jiragen sama, Mr Festus Keyamo ya bayyana dalilan da suka sa gwamnatin tarayya ta mayar da wasu ofisoshin hukumar FAAN zuwa Legas daga Abuja.

Mr Keyamo ya ce mayar da hedikwatar hukumar Legas zai zama abun da ya fi alkairi ga Najeriya musamman ganin cewa ana tafiyar da kudaden al'umma a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel