Ku Daina Cusa Ƙiyayyar Tinubu a Zukatan Ƴan Najeriya, Famuyibo Ya Gargadi Shugabannin Arewa

Ku Daina Cusa Ƙiyayyar Tinubu a Zukatan Ƴan Najeriya, Famuyibo Ya Gargadi Shugabannin Arewa

  • An gargadi shugabannin Arewa da su kauracewa kalaman tunzurarwa da cusa ƙiyayyar Tinubu a zukatan'yan Najeriya
  • Chief Reuben Famuyibo ya yi gargadin yayin da yake martani kan halin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da ake fama da su a kasar
  • Famuyibo ya yi ikirarin cewa gwamnatin Buhari ce ta jefa 'yan Najeriya cikin talauci ba Tinubu ba, don haka 'yan Arewa ba su da bakin magana

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma lauya, Cheif Reuben Famuyibo, ya gargadi shugabannin Arewa da su daina cusa ƙiyayyar Shugaba Tinubu a zukatan 'yan Najeriya.

Famuyibo, a tattaunawa da jaridar The Nation a ranar Litinin, ya ce kalaman shugabannin Arewa na iya jawo zaune tsaye a kasar.

Kara karanta wannan

Atiku ya fadi yadda Tinubu ya haddasa tashin Dala da rugujewar tattali a wata 8

Reuben Famuyibo ya kare gwamnatin Tinubu
Reuben Famuyibo, ya gargadi shugabannin Arewa kan kalaman tunzurwar da suke yi akan Tinubu. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Facebook

Famuyibo ya koka kan cewa sarakunan gargajiya, 'yan siyasa da malaman addini sun yi wa gwamnatin Tinubu 'caa' alhalin ba su ce 'uffan' ba a gwamnatin Buhari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalaman 'yan Arewa na neman wuce gona da iri - Famuyibo

Dan siyasar dan asalin jihar Ekiti, ya ce shugabannin Yarabawa sun fara hasala da munanan kalaman 'yan Arewa kan gwamnatin Tinubu, kuma ba za su ci gaba da yin shiru ba.

Ya ce:

"Babu laifi don 'yan Najeriya sun yi korafi kan halin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwar da ake ciki a kasar, amma kalaman shugabannin Arewa na neman wuce gona da iri.
"Babu ta yadda za a yi su fake da halin da ake ciki su rinka cin dunduniyar Shugaba Tinubu, wannan cusa ƙiyayyar shugaban kasar ne karara a zukatan 'yan Najeriya."

Buhari ne ya jefa Najeriya cikin talauci - Famuyibo

Kara karanta wannan

"Da tallafi, babu wuta": Shehu Sani ya magantu kan shirin Tinubu na janye tallafin wutar lantarki

Famuyibo ya kuma zargi shugabannin Arewa da nuna bambancin kabila da addini musamman kan batun dauke FAAN da CBN daga Abuja zuwa Legas.

"Muna so mu ja hankalinsu kan cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya jawo lalacewar tattalin arzikin kasar, kuma shi ne ya jefa talauci ba wai Shugaba Tinubu ba.
"Ya zama wajibi su kawo karshen kalaman tunzurarwa da suke yi da kuma tunanin cewa su kadai ne ya kamata su yi mulki."

A cewar tsohon dan takarar shugaban kasar.

Kuskuren da Tinubu ya tafka tun kafin hawa mulki - Farfesa Dandado

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa Farfesa Kabiru Isa Dandado ya koka kan yadda Najeriya ya fada cikin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa.

Farfesa Dandado ya ce tun farko Shugaba Tinubu ya tafka kuskure na janye tallafin man fetur tun kafin ma ya shiga fadar shugaban kasa.

Dandado, wanda kuma tsohon kwamishinan kudi ne na jihar Kano, ya ce tsare-tsaren gwamnatin Tinubu sun jawo tsadar abinci ka kayan masarufi a kasar

Asali: Legit.ng

Online view pixel