Gwamnatin Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta karbi sama da naira biliyan 100 daga cibiyoyin hada-hadar kudi a matsayin karin haraji ga ayyukan da suka yi a shekarar 2023.
Salihu Muhammad Lukman ya yi magana a kan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ya ce da farko Tinubu ya samu karbuwa, yanzu an koma irin mulkin Muhammadu Buhari.
Bayan shekara uku, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya janye dokar da ya kakabawa masu hada-hadar sulallan 'crypto' tare da ba bankunan umurni kan hakan
Gwamnatin tarayya ta sanar da lokacin da za ta saki sunayen wadanda za su ci moriyar shirin shugaban kasa na tallafin naira dubu hamsin a watan Janairu 2024.
Uwar gidan shugaban kasa Tinubu ta sanya farin ciki a zukatan dattawa 250 a jihar Katsina bayan ba su tallafin naira dubu 100 duk mutum daya don rage radadin talauci
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun hutu domin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara. Ministan harkokin cikin gida ne ya sanar da hakan a madadin gwamnati.
Gwamnatin kasar Faransa ta kafa sabuwar doka kan daliban Najeriya da sauran kasashen duniya zuwa da iyalansu kasar saboda wasu dalilai masu muhimmanci.
Gwamnatin Najeriya ta zabtare farashin ababen hawa tare da mayar da jirgin kasa ya zamo kyauta a yayin bikin Kirsimeti da sabuwar shekara kasar..
Mai girma shugaban Najeriya, ya ce mutane za su ga cigaban da za a samu a badi. Daga shekarar 2024, gwamnatin tarayya ta ce jama’a za su fara kurban jar miya.
Gwamnatin Najeriya
Samu kari