Bayan Mutuwar Akeredolu, Jigon APC Ya Bayyana Wanda Za a Rantsar a Matsayin Sabon Gwamnan Ondo

Bayan Mutuwar Akeredolu, Jigon APC Ya Bayyana Wanda Za a Rantsar a Matsayin Sabon Gwamnan Ondo

  • Da alama mutuwar Gwamna Rotimi Akeredolu ta bayar baya da kura a fannin da ya shafi siyasar jihar Ondo
  • Wani jigo a jam’iyyar APC ya bayyana cewa ana shirin rantsar da mukaddashin gwamna Lucky Aiyedatiwa a matsayin sabon gwamnan jihar
  • Kwanan nan ne aka nada Aiyedatiwa a matsayin mukaddashin gwamnan jihar Ondo bayan Akeredolu ya shafe sama da watanni biyar baya zaune a jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Ondo - Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo, ya rasu yana da shekaru 67, al’amarin da ya kai ga sake shirya siyasa a jihar mai lakabi da "hasken rana".

Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar ya shaidawa The Punch cewa ana shirin rantsar da mukaddashin gwamnan, Lucky Aiyedatiwa.

Kara karanta wannan

Abubuwa 28 da ya kamata ku sani game da marigayi gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu

Za a rantsar da sabon gwamna a Ondo
Za a rantsar da mataimakin gwamnan Ondo matsayin sabon gwamnan bayan mutuwar Akeredolu. Hoto: Rotimi Akeredolu, Lucky Aiyedatiwa
Asali: Twitter

Rikicin siyasa a Ondo kan rashin lafiyar Akeredolu

A baya dai, Aiyedatiwa ya kasance mukaddashin gwamnan jihar, bayan da aka dade ana fafata rikicin siyasa da ‘yan majalisar jihar, Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayi Gwamna Akeredolu ya shafe watanni uku yana jinya a kasar Jamus, inda jama'a suka yi ta cece-kuce kan ko zai iya jan ragamar jihar.

Gwamna Akeredolu a sa'in ya dawo Najeriya amma ya zauna a gidansa na kashin kansa dake Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Yadda aka nada Aiyedatiwa matsayin mukaddashin gwamnan Ondo

Akeredolu dai ya yi yunkurin mulkin jihar ne daga Ibadan, amma wasu ‘yan majalisar na da ra’ayin cewa ya kamata a rantsar da Aiyedatiwa a matsayin mukaddashin gwamnan jihar.

Wannan al’amari ya sanya akasarin ‘yan majalisar suka zabi tsige mataimakin gwamnan, amma shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani, kuma masu ruwa da tsakin sun amince a ci gaba da kasancewa a haka.

Kara karanta wannan

Labari da Dumi-Dumi: Gwamnan Najeriya ya mutu yana jinya a asibitin kasar waje

A farkon watan Disamba ne lafiyar gwamnan ta kara tabarbarewa, kuma majalisar dokokin jihar ta zabi a rantsar da Aiyedatiwa a matsayin mukaddashin gwamnan jihar.

Gwamna Akeredolu ya riga mu gidan gaskiya

A safiyar yau ne muka ruwaito maku rasuwar gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, bayan shan fama da rashin lafiya.

Rahoton Vanguard ya ce Marigayin ya mutu ne a hannun likitocin gwamnati da ke Legas a safiyar ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel