Gwamnati Za Ta Saki Sunayen ’Yan Najeriya da Za Ta Ba Tallafin N50k a 2024

Gwamnati Za Ta Saki Sunayen ’Yan Najeriya da Za Ta Ba Tallafin N50k a 2024

  • Gwamnatin tarayya ta sanar da lokacin da za ta saki sunayen wadanda za su ci moriyar shirin shugaban kasa na tallafin naira dubu hamsin
  • Minsitar jin kai da kawar da fatara, Betta Edu ta sanar da cewa a watan Janairu kowa zai san wanda ya shiga cikin shirin da aka fara a watan Disamba
  • Gwamnatin Tinubu ta kawo wannan shiri don rage wa 'yan Najeriya radadin cire tallafin man fetur, musamman talakawa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Betta Edu, ministar jin kai da kawar da fatara ta yi alkawarin wallafa sunayen wadand za su ci gajiyar shirin shugaban kasa na naira dubu hamsin.

Bettu Edu ta tabbatar da sakin sunan a watan Janairu a wata hira da Channels TV’s a ranar Juma'a inda ta ce shirin zai rage radadin cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Ina za ki damu: Mata ta hada baki da mijinta sun hallaka abokinsa a Kano

Gwamnati za ta saki sunayen 'yan Najeriya, shirin tallafin N50,000
Gwamnati ta ce watan Janairu 2024 za ta saki sunayen 'yan Najeriya da za su ci gajiyar tallafin N50,000. Hoto: @officialABAT, @edu_betta
Asali: Getty Images

Tsare tsaren da gwamnati ta yi kan shirin tallafin shugaban kasa

Daily Trust ta ruwaito Minista Edu na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Muna so mu zama masu baje komai a fili, za mu saki sunayen wadanda za su ci gajiyar shirin don ba al'ummar duniya damar dubawa, hakan zai nuna gaskiya da rikon amana a shirin.
"Mun yi amfani da duk wata fasaha da ake bukata, muna da na'uori masu aiki ba daukewa, wasu na gwamnati wasu na 'yan kasuwa kamar fasahar remita da za ta rinka biyan kudin kai tsaye."

Yaushe za a saki sunayen wadanda za su ci gajiyar shirin?

A cewar ministar, gwamnati za ta yi amfani da 'remita' wajen cire kudi daga asusun CBN TSA zuwa asusun wadanda za su ci gajiyar shirin, babu bukatar sai ya bi ta hannun wani.

Kara karanta wannan

Jerin garuruwan da matafiya za su samu ragin 50% da zababbun kamfanonin sufuri da ke cikin tsarin

Edu ta ce:

"Yanzu muna ci gaba da daukar sabbin mutane a cikin shirin. Muna fatan talakawa da ke fama da matsalar kudi su nemi shiga shirin.
"A watan Janairu za mu wallafa sunayen wadanda za su ci gajiyar shirin gwamnatin tarayyar don 'yan Najeriya su san wadanda suka samu shiga."

Tinubu ya dawo da shirin ciyar da dalibai abinci, ya yi sabon tsari

A wani labarin, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umurnin dawo da shirin ciyar da dalibai domin magance yawan daliban da ke gararamba a garuruwan Najeriya.

Shugaban kasar ya kuma ba da umurnin a cire shirin ciyarwar daga ma'aikatar jin kai a mayar da shi karkashin ma'aikatar ilimi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel