Hutun Kirsimeti: Tinubu Ya Zabtare Rabin Farashin Ababen Hawa, Tafiya a Jirgin Kasa Kyauta Ne

Hutun Kirsimeti: Tinubu Ya Zabtare Rabin Farashin Ababen Hawa, Tafiya a Jirgin Kasa Kyauta Ne

  • Gwamnatin Najeriya ta mayar da jirgin kasa ya zamo kyauta don saukaka wa 'yan Najeriya da ke hsirin bikin Kirsimeti da sabuwar shekara
  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya kuma zabtare farashin ababen hawa da kaso 50% daga ranar 21 ga watan Disamba 2023 zuwa ranar 4 ga watan Janairu 2024
  • A cikin wata sanarwa daga hadimin Tinubu ta fuskar watsa labarai, Bayo Onanuga, shugaban kasar ya yi wa 'yan Najeriya fatan yin bukukuwa lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zabtare farashin ababen hawa da kaso 50% a tafiye-tafiyen jiha zuwa jiha a fadin Najeriya.

Haka zalika, shugaban kasar ya ba da umurnin cire kudin hawan jirgin kasa, wanda ke nufin matafiya za su hau jirgin kasa kyauta.

Kara karanta wannan

Harin sojojin Najeriya kan farar hula: Miyetti Allah ta kafa wa Tinubu wani muhimmin sharadi

Tinubu ya zabtare ababen hawa saboda kirsimeti
Tinubu ya zabtare farashin ababen hawa, jirgin kasa ya koma kyauta saboda bikin kirsimeti da sabuwar shekara
Asali: Facebook

Tinubu ya dauki wannan matakin ne don saukaka wa 'yan Najeriya a yayin da su ke shirye-shiryen bikin kirsimeti da sabuwar shekara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai tallafawa shugaban kasar ta fuskar watsa labarai, Bayo Onanuga ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter.

Onanuga ya ya ce sabon farashin ababen hawan da kuma cire kudin jirgin kasa zai fara aiki daga ranar 21 ga watan Disamba 2023 zuwa ranar 4 ga watan Janairu, 2024.

A mayar da ilimi kyauta a Najeriya - Wakilin Dalibai ya roki Tinubu

An yi kira ga Shugaba Tinubu da ya ba da umurnin janye batun karin kudin jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire (UTME) don bunkasa ilimi a kasar.

Wakilin Daliban Durbin Katsina, Sanusi Yau Mani ya yi wannan kiran a zantawarsa da Legit Hausa inda ya ce ya kamata ilimi ya zama kyauta a Najeriya.

Sanusi Mani ya ce har sai an samar da ilimi ga matasa ne za a kawo karshen ta'addanci a kasar, yana mai cewa bai kamata ayi wasa da harkar ilimi ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel