Shugaba Bola Tinubu Ya Tsaida Lokacin da Mutane Za Su Fara Jin Dadin Gwamnatinsa

Shugaba Bola Tinubu Ya Tsaida Lokacin da Mutane Za Su Fara Jin Dadin Gwamnatinsa

  • Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashi cewa a shekarar 2024 da za a shiga, abubuwa za su kara kyau a Najeriya
  • Shugaban kasa ya dauki wannan alkawari ne a wajen kaddamar da ofishin da hukumar EFCC ta bude a Enugu
  • Nuhu Ribadu ya wakilci Mai girma shugaban Najeriya, ya ce mutane za su ga cigaban da za a samu a badi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A jiya aka ji shugaba Bola Ahmed Tinubu yana maganar Najeriya a karkashin jagorancinsa da kuma inda aka dosa a yau.

The Nation ta ce Bola Ahmed Tinubu ya tabbatarwa al’umma cewa zuwa shekara mai zuwa za a fara ganin tasirin ayyukansa.

Shugaba Bola Tinubu
Bola Tinubu tare da Shugabannin tsaro Hoto: @NuhuRibadu
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya yabi jami'an tsaro

Kara karanta wannan

Tsohon Ministan Buhari ya ci gyaran Shugaba Tinubu a kan abubuwa 2 da ya aikata a ofis

Sabon shugaban na Najeriya ya yabawa jami’an tsaro a kan kokarin da su ka yi wajen inganta zaman lafiya a jihohin kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya ce ana fatattakar ‘yan ta’addan Boko Haram da ‘yan bindigan da su ka addabi jama’a na tsawon shekara da shekaru.

Hukumar EFCC ta samu sabon ofishi

Shugaban kasar ya yi wannan jawabi wajen bude sabon ofishin hukumar EFCC a Enugu.

Rahoton ya ce mai ba shugaban kasa shawara a kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya wakilce shi wajen kaddamar da ofishin.

A jawabin da ya gabatar, NSA ya jinjinawa kokarin Ola Olukoyede da mutanensa.

Jawabin Nuhu Ribadu a madadin Tinubu

"Muna bukatar abubuwa su yi aiki a kasarmu. Muna bukatar abubuwa su gyaru. Muna so mu yi abubuwan da su ka dace.

Kara karanta wannan

Duka yarjejeniya 8 da aka dauka wajen sasanta Wike da Gwamna Fubara a Aso Rock

Kuma shi (shugaban kasa) yana bakin kokarinsa wajen yin haka. Abubuwa na canzawa. A 2024, a jira a ga abin da zai faru."

- Nuhu Ribadu

Blueprint ta ce Olukayode ya dauki alkawari za su ga bayan ‘yan damfarar Najeriya.

Shugaban kasa Tinubu ya sha alwashi ba zai yi wasa da jin dadi da walwala ma’aikatan EFCC masu yaki da rashin gaskiya ba.

Siminalayi Fubara ya fusata Bola Tinubu

Shugaban kasa Bola Tinubu ya nuna takaicinsa a kan yadda gwamnan Ribas ya rusa ginin ‘yan majalisar dokoki kan sabanin siyasa.

Tinubu ya caccaki Gwamna Siminalayi Fubara a taron sulhu da aka yi da Nyesom Wike wanda shi Nuhu Ribadu ya samu halarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel