Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Sun Yi Bikin Kirsimeti Ba Tare da Albashin Disamba Ba

Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Sun Yi Bikin Kirsimeti Ba Tare da Albashin Disamba Ba

  • Gwamnatin tarayya bata biya ma'aikata albashin watan Disamba kafin bikin Kirsimeti ba
  • Ma'aikata sun koka cewa rashin kudi ya hana su gudanar da bukukuwan bana cikin jin dadi
  • Wani ma'aikacin jami'a ya ce tsawon watanni shida kenan basu samun albashinsu kafin karshen wata

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Galibi ba'a yi bikin Kirsimeti cikin jin dadi ba kamar yadda aka saba a gidajen ma'aikatan gwamnatin tarayya da dama, inda aka samu karancin dafe-dafen abinci da ziyarce-ziyarce saboda tsaiko da aka samu wajen biyan albashin watan Disamban 2023.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, ma'aikata da ke aiki a hukumomin tattara kudaden shiga kamar su NNPC, NPA, NIMASA, NCC, CBN, da FIRS ne kadai suka samu albashinsu na Disamba.

Kara karanta wannan

Wani bam da aka dasa ya tashi, ya yi ajalin wani jami'in hukumar NSCDC a jihar Arewa

Ma'aikata za su yi bikin Kirsimeti ba albashi
Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Sun Yi Bikin Kirsimeti Ba Tare da Albashin Disamba Ba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ma'aikata sun yi Kirsimeti cikin rashin kudi

Ma'aikatan sun koka cewa tsaikon da aka samu wajen biyan albashin ya shafi shagalinsu na Kirsimeti kuma yana iya kuma yana iya yin mummunan tasiri ko da a watan Janairu lokacin da makarantu za su koma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani malami a jami'ar Abuja ya ce:

“Babu wani uzuri ko kadan, matagana ta gaskiya. Sun cire tallafin mai, sun ce suna tara kudade tun watan Yuni. Sama da watanni shida kenan amma ba kasafai muke samun albashi kafin karshen wata ba.
“Na samu albashin watan Nuwamba a sati na biyu na watan Disamba. Yanzu da yake karshen shekara kuma lokacin Kirsimeti ne, mun yi tunanin za su biya mu kusan 20 ko 22. Abin bakin ciki, ba su yi ba."

Wani ma’aikaci ya ce bai taba samun tsaiko a albashin watan Disamba ba a gwamnatin da ta gabata.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin da suka bai wa ma'aikatan jihohinsu kyautar N100,000 a ƙarshen 2023

"Duk da rashin kokarin gwamnatocin baya, ba zan iya tuna lokacin da aka jinkirta biyan albashin watan Disamba ba.
"Ta yaya za ka yi farin ciki alhalin ba za ka sanya iyalinka farin ciki ba a wannan biki?" wani malamin jami'a ya tambaya.

Wata lackara a jami’ar FUT Minna ta fada ma jaridar Legit cewa tunda take bata taba bikin Kirsimeti mara armashi irin wannan ba saboda babu kudi.

Ta ce:

“Gaskiya mun yi Kirsimetin bana a bushe sam babu armashi. Gari babu kudi ga shi har aka sha shagali aka gama gwamnati bata biya mu albashi ba sai daga baya.
“Haka muka yi bikin cikin kame-kame, har addu’a na dunga yi kada Allah ya kawo mun ko wani bako saboda me zan ba shi? Allah dai ya kyauta.”

Ofishin Akanta Janar ya magantu

Kakakin Ofishin Akanta Janar na Tarayya, Malam Bawa Mokwa ya tabbatar da rashin biyan albashin watan Disamba da gwamnati bata yi ba kafin bikin Kirsimeti.

Kara karanta wannan

Rundunar Sojojin Najeriya ta kama jami’inta kan mutuwar direban babban mota a Borno

Mokwa ya ce nan ba da dadewa ba ma’aikata za su fara samun albashinsu saboda ana bisa kan aiki.

Sai dai wani babban jami’in gwamnatin kasar ya bayyana cewa an samu tsaikon ne sakamakon wata matsala da aka magance.

Ya kara da cewa ma’aikata za su karbi albashinsu kafin karshen ranar Litinin 25 ga watan Disamba.

Musulmai sun taya Kiristoci murna

A wani labarin, mun ji cewa wasu al'ummar Musulmai a jihar Bauchi sun ziyarci cocin Yalwan Kagadama da ke Bauchi a ranar Litinin, 25 ga watan Disamba, don raya Kiristoci murnar zagayowar ranar haihuwar Yesu.

Musulman wadanda sun yarda cewa hadin kai tsakanin addinan guda biyu da da muhimmanci don ci gaban kasar don haka suka yi kira ga kulla dangantaka mai kyau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel